MDD ta ce ta samu tabbacin hada kan sojoji dubu 15 ga Libanon | Labarai | DW | 26.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta ce ta samu tabbacin hada kan sojoji dubu 15 ga Libanon

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya nunar da cewa rundunar kiyaye zaman lafiya da za´a girke a Libanon zata samu yawan sojoji dubu 15 da ake bukata. Bayan wata ganawa da ministocin harkokin wajen kasashen KTT a birnin Brussels, Annan yayi maraba da alkawuran da kasashen Turai suka dauka na ba da kaso mafi yawa ga dakarun na MDD. A jiya juma´a Faransa, Italiya, Spain da wasu kasashen Turai sun yi alkawarin tura sojoji kimanin dubu 7 ga rundunar ta UNIFIL da za´a fadada ta. Jamus kuwa zata ba da gudunmawa ne a fannin mayakan ruwa a aikin kiyaye zaman lafiya na GTT, to sai dai ba ta fayyace iya yawan taimakon da zata bayar din ba. Faransa ce zata jagoranci rundunar ta MDD har zuwa watan fabrairu lokacin da zata mikawa Italiya ragamar. Gwamnatin Libanon ta mika godiyarta ga KTT dangane da wannan taimako.