MDD: Ta ce kisan Rohingyas da gangan ne.
October 11, 2017Talla
Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kisan wani abu ne da aka tsara da nufin kawar da tsirarun kabilun Musulmi na Rohingyas baki daya daga kasar ta Bama. Masu yin binciken sun yi tambayoyi ga gomai na jama'ar da suka tsere daga yankin Rakhine zuwa Bangladesh bayan barkewar tashin hankalin a cikin watan Augustan da ya gabata