Mdd ta bukaci Sudan ta amince da sojin kiyaye zaman lafiya na Mdd | Labarai | DW | 02.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mdd ta bukaci Sudan ta amince da sojin kiyaye zaman lafiya na Mdd

Babban magatakardar Mdd, Mr Kofi Anan yace dole ne ayi kokarin janyo hankalin mahukuntan Sudan amincewa da bataliyar sojin kiyaye zaman lafiya ta Mdd izuwa yankin Darfur, dake Kudancin kasar.

Mr Anan , ya fadi hakan ne a jiya yayin da yake gabatar da jawabi a gaban taron kwamitin sulhu na Mdd a can birnin New york na Amurka.

Mdd dai na kokarin ganin an tura bataliyar soji zambar dubu 17 izuwa yankin na Darfur, don taimakawa wajen kawo karshen tashe tashen hankula da rikice rikice da yankin yake fama dashi.

Ya zuwa yanzu dai akwai dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na kasashen Africa a kalla dubu shidda da dari biyu a yankin na Darfur.