1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta bukaci Jammeh ya bada hadin kai

December 13, 2016

Wata tawaga mai karfi ta shugabannin yammacin Afirka za ta kai ziyara Gambiya domin shawo kan shugaba Yahya Jammeh ya amince da kaddara ya mika ragamar mulki cikin kwanyiyar hankali.

https://p.dw.com/p/2UBKJ
USA UN-Sicherheitsrat tagt in New York zu Syrien
Wakilan kwamitin sulhun Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Getty Images/AFP/D. Reuter

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh ya gana da tawagar masu shiga tsakani daga kasashen duniya wadanda suka tashi zuwa Banjul domin rarrashinsa ya mika ragamar mulki.

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari da shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf da shugabannin Saliyo da na Ghana da kuma manzon Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afirka Muhammed Ibn Chambers za su sauka birnin banjul a yau Talata domin ganawa da shugaban.

Kwamitin sulhun Majalisar ya bukaci shugaba Jammeh ya bada hadin kai ga tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya da ta kungiyar raya ci gaban kasashen yammacin Afirka  ECOWAS  domin cimma masalaha cikin ruwan sanyi.