MDD ta bayyana bukatar bawa Palasdinawa kasarsu | Labarai | DW | 02.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta bayyana bukatar bawa Palasdinawa kasarsu

Zauren mdd ya amince da kudurorin guda shida dake marawa yankin palasdinawa baya,duk da adawa da Amurka da Izraela sukayi kann batutuwan,wanda ke bayyana yadda zauren mdd dake mahawara a kowace shekara,ke ganin cewa ,lokaci yayi da zaa bawa palasdinawa yancin cin gashin kansu.A karshen mahawara ta kwanaki uku,wakilan kasashe 192,dake cikin mdd ,sun jaddada hakki daya rataya a wuyan majalisar ,adangane da batun bawa alummomin palasdinu yantacciyar kasarsu.Adangane da matsalolin dake addabar yankin kuwa,wakilan sunyi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a ranar 26 ga watan daya gabata a zirin gaza,tare da kira ga bangarorin biyu dasu darajawa yarjejeniyar,wanda shine kadai zai jagoranci gano bakin zaren kawo karshen rikicin dake addaman yankin.Wakilin Palasdinu a zauren mdd Riyad Mansour,yace kasashe 157 ne suka kada kuriun goyon bayansu wa Palasdinawan,ayayinda 7,sukayi adawa,kana wasu kasashe 10 da basu bayyana ba.