MDD ta ba da tabbaci Koriya Ta Arewa zata rufe tashar nukiliyar ta | Labarai | DW | 30.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta ba da tabbaci Koriya Ta Arewa zata rufe tashar nukiliyar ta

Bayan ziyarar da suka a kasar KTA kwararrun masana na MDD sun nuna kyakkyawan fatan cewa nan ba dadewa ba kasar mai bin tsarin kwaminisanci zata rufe tashar nukiliyar Yongbyon da ake takaddama a kai. To sai dai shugaban tawagar ta MDD, Olli Heinonen ya fada a birnin Beijing cewa har yanzu ba´a sanya lokacin da za´a rufe tashar ba. A shekaranjiya alhamis Heinonen da tawagarsa suka kai ziyara a tashar nukiliyar ta Yongbyon. A tattaunaar da ta yi da Amirka, China, Japan da kuma KTK, gwamnatin KTA ta nuna aniyar kawo karshen shirin ta na nukiliya. Sannan ita kuma saka mata da taimakon tattalin arziki da na jin kai. A yau asabar´dai ne KTK zata fara tura kayan abinci ga KTA.