MDD ta amince da tura dakarun Afrika zuwa Somalia | Siyasa | DW | 07.12.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MDD ta amince da tura dakarun Afrika zuwa Somalia

Shugaba Abdullahi Yusuf na Somalia

Shugaba Abdullahi Yusuf na Somalia

Komitin sulhun Mdd ya cimma kudurin amincewa da tura dakarun kasashen Afrika zuwa Somalia domin tallafawa gwamnatin rikon kwarya na wannan kasa dake fama da rikici.

Wannan kuduri da komitin sulhun mdd ya cimma na nufin samar da kyakkyawar kariya wa jamian gwammnatin rikon kwarya dake da matsugunninsu a Baidoa,wadanda kuma ke fuskatar barazanar gamayyar kungiyoyin kotunan musulmi.

To sai dai da cimma wannan kuduri ,ayau din kungiyoyin musulmin somalian suka mayar da martani dacewa ,matakin na mdd bazai haifar da komai face dada ruru wutar rikici dake cigaba da ci a kasar dake kahon Afrika,wadda kuma ke cikin shirin kota kwana a dangane da fadawa yakin basasa.

A nata bangare kuwa,gwamnatin rikon kwaryan tayi maraba da wannan kuduri na majalisar dunkin duniya na samar mata kariyar soji,inda ta mika godiyarta ta musamman wa Amurka wadda ta taka rawar gani wajen cimma wannan kuduri.

Duk da cewa shigar da dakarun kiyaye zaman lafiya na ketare zuwa cikin saomaliyan zai iya haifar da barazanar kwararan yan tarzoma daga ketare,a jiya laraba nedai komitin sulhun mdd ya amince da kudurin shigar da dakarun kasashen Afrika zuwa cikin Somallia,domin taimakawa gwamnatin Shugaba Abdullahi Yusuf,na jeka nayika.

Gwmantin shugaba yusuf din dai na muradin ganin cewa somaliyar ta samu zaunanniyar gwamnatin kasa,wadda kasar ta rasa tundaga shekarata 1991,musamman karbe madafan ikon babban birninkasar ta mogadishu da wasu manyan garuruwan dake kudanci,wadanda gamayyar kungiyoyin musulmi suka rike da madafan ikonsu tun daga watan yunin daya gabata.

Daga cikin batutuwa da mdd ta zartar dai shine har yanzu takunkumin nan na shigab makamai cikin kasar zai cigaba da aiki,sai dai kawai a bangaren dakarun kiyaye zaman lafiyan kasashen Afrika da zasu shiga wannan kasa,wadanda aikinsu na farko zai kasance kulawa da harkokin tsaro.

To sai dai a nasu bangarern kungiyoyin musulmin basu hangi wannan matakai a matsayin mai haifar da tudun dafawa rikicin somalian ba.Kakakin kungiyar Abdirrahman Ali Mudey,yace amincewa da mdd tayi na shigar da makamai cikin wannan kasa bazai haifar da komai ba face kara ruruta wutan rikicin wannan kasa.

Su kuwa jamian diplomasiyya gani suke cewa,wannan maganace kadai ta siyasa domin samarda zaman lafiya fiya da aiwatar dashi.Kana a bangaren Afrika,barazanar kudaden daukan nauyin sojojin da yiwuwar barkewan yakin basasa zai hanasu yin wani motsi a halin yanzu.

 • Kwanan wata 07.12.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtxB
 • Kwanan wata 07.12.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtxB