MDD na neman agajin dala million 60 a Iraki | Labarai | DW | 08.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD na neman agajin dala million 60 a Iraki

Hukumar kula da yan gudun hijra ta ta mdd tayi kira ga kasashen duniya da hukumomi na agaji,dasu bada gudummowan dala million 60,domin agajin gaggawa wa yan Iraki kimanin millin 1 da dubu dari 7 ,da suka rasa matsugunnensu sakamakon karuwar tashe tashen hankula da kasar ke fama dasu.Hukumar kula da yan gudun hijiran ta kiyasta cewa a kowane wata,a kalla yan Irakin daga dubu 40 zuwa dubu 50 ne ke tserewa daga gidajensu.Adangane da wannan kiyasi ne tace awannan shekara kadai kimanin yan Irakin million 2.3 zasu rasa matsugunnensu a wannan shekara kadai.Ayayinda wasu kimanin miliyan 2 sukayi gudun hijira zuwa wasu kasashen ketare,da suka hadar da Jordan da Syria da Masar.