MDD: Mutane miliyan 20 na fama da yunwa | Labarai | DW | 11.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Mutane miliyan 20 na fama da yunwa

Jami'in ba da agajin gaggawa a Majalisar Dinkin Duniya Stephen O'Brien, ya ce al'ummar kasashen da ke fama da rigingimu da yake-yake na cikin mawuyacin hali na yunwa da karancin abinci.

Jami'in ba da agajin gaggawa na MDD ya ce, ana bukatar biliyoyin dala domin tallafa wa mutane miliyan 20 da ke fuskantar barazanar yunwa da karancin abinci a a kasashen Yemen da Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Da ya ke gabatarwa kwamitin sulhu sakamakon ziyararsa zuwa yankunan rikicin, Stephen O'Brien ya ce, MDD da kawayenta na shirye wajen fuskantar wannan lamari, sai dai suna bukatar kudi da izinin shiga wadannan wurare.

" Lamarin ya yi munin da ba'a taba ganin irinsa ba. Yunwar da ke kasar Sudan ta Kudu alal misali, mutanen da suka haifar da rigingimun ne suka janyo ta. Amma matsalar kasar Somaliya za'a iya shawo kanta, sai Yemen babu damar kai kayayyakin agaji, duk da alkawura da abokan fadan suka yi a baya".