1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ka iya tura dakaru a yankin kan iyaka tsakanin Chadi da Sudan

October 28, 2006
https://p.dw.com/p/Bue5
Dan Halutz
Dan HalutzHoto: AP
A dangane da bazuwar rikicin lardin Darfur na yammacin Sudan, MDD na duba yiwuwar fadada aikin zaman lafiyar ta zuwa kasar Chadi makwabciyar Sudan. Wakilin MDD a yankin Jean-Marie Guehenno ya ce ana iya mikawa kwamitin sulhun MDD batun na girke wata tawagar sa ido ko ma dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin kan iyakar Chadi da Sudan. A yau dai gwamnatin Chadi ta zargi mayakan sama na Sudan da kai hare hare kan wasu kauyukanta 4 dake kan iyakarta da lardin Darfur. To sai dai babu labari game da rayukan da suka salwanta sakamakon hare haren. Sudan da Chadi dai na zargin juna da goyawa ´yan tawayen kasashen biyu baya.