Mazauna yankin fatakwal sun fara tserewa | Labarai | DW | 17.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mazauna yankin fatakwal sun fara tserewa

Rahotanni daga birnin Fatakwal a taraiyar Najeriya sunce mazauna birnin sun fara tserewa yayinda dakarun soji suka fara kwarara zuwa yankin kwana guda bayan fada tsakanin sojoji da membobi wata kungiyar tsageran yankin.

Mazauna kusa da sansanin sojin da akayi bata kashin na jiya sunce suna tsoron sake barkewar sabon fada ne a yankin kodayake babu rahoton ainihin yawan mutanen da suka tsere sai dai kuma jamaa da dama sunyi anfani da lafawar alamura na yau domin gujewa sake barkewar tashe tashen hankulan.