1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Homosexuelle Afrika

Tijani LawalFebruary 18, 2010

Ana dai fama da matsaloli da dama a sassa daban-daban na duniya dangane da maza masu neman maza ko kuma mata dake neman 'yan uwansu mata.

https://p.dw.com/p/M4oI
Masu zanga-zangar neman tabbatar da haƙƙin maza masu neman maza a Kampala ta UgandaHoto: AP

Bisa ga ra'ayin Thomas Mösch a cikin sharhinsa dai wajibi ne ƙasashen yammaci su riƙa katsalandan a duk inda ake take haƙƙin maza dake neman maza a ƙasashen Afirka da na Asiya.

Homosexuelle aus ganz Indien feiern am Sonntag, den 28. Juli 2009 ausgelassen die "Delhi Queer Parade Foto: UNI
Jerin gwanon maza masu neman maza a Delhi ta IndiyaHoto: UNI

Ya ce a ƙasar Malesiya yanzu haka an gufanar da wani jami'in siyasar 'yan adawa gaban kuliya saboda zarginsa da laifin neman wani ɗan uwansa namiji. A wasu ƙasashe na Musulmi akan zartar da hukuncin kisa akan maza dake neman 'yan uwansu maza. A ƙasar Uganda dake gabacin Afirka jami'an siyasa sun ƙuduri niyar tsaurara dokar haramcin dake akwai domin mayar da ita ta hukuncin kisa. A mayar da martani ƙasashen Turai suka yi mata barazanar matakai na takunkumi. Galibi waɗannan ƙasashe kan musunta duk wani zargin da za a yi musu game da farautar maza masu neman 'yan uwansu maza suna masu kafa hujja da al'adu ko addini, wanda babu wata ƙasa ta ƙetare dake ikon yi musu shisshigi a ciki. Masu neman haramtawa ko kuma ƙara tsaurara dokokin da suka shafi dangantakar namiji da namiji a ƙasashen Afirka da na Asiya su kan zargi masu sukan lamirinsu da wani yunƙuri na wajabta musu abin da suka kira ɗabi'un ƙasashen yammaci. Wato ke nan rikici game da haƙƙin maza masu neman 'yan uwansu maza lamarin ne da ya shafi banbancin al'adu tsakanin Turai da sauran sassa na duniya. Sau tari akan shigo da maganar addini a a ciki, inda galibi akan samu daidaituwa tsakanin malamai na musulmi da na kirista. Amma fa wannan iƙirarin ba daidai ba ne. Saboda hatta a ƙasashen yammaci akwai banbance-banbance a game da ma'amalla da maza masu neman maza ko kuma mata dake neman 'yan uwansu mata, a yayinda a wasu sassa na duniya da basu da wata alaƙa da al'adun ƙasashen yammaci maganar soyayya tsakanin namiji da namiji ko mace-da-mace bata ci musu tuwo a ƙwarya. A haƙiƙa ma dai a ƙasashe da dama na Afirka da Asiya dokokin da 'yan mulkin mallaka suka gabatar a zamanin baya game da 'yan luwaɗi da maɗigo su ne ke ci a har yanzu. A saboda haka bai kamata ƙasashen yammaci su yarda a yaudare su da ire-iren hujjar da ake kafawa ba. Maganar al'adu ko addini ba ta isa zama hujjar take haƙƙin wani rukuni na 'yan ƙasa ba. Gwamnati na da ikon ƙayyade haƙƙin mutane ne idan take-takensu zai haifar da wata illa ga al'uma. Amma fa alaƙa ta soyayya bisa raɗin kai tsakanin mutane biyu ba ta haifar da illa ga kowa. Kowace ƙasa tana da ikon haramtawa ko halasta aure tsakanin maza ko mata, amma maganar ɗaure su a kurkuku ko zartar musu da hukuncin kisa, abu ne da yayi daura da manufar girmama haƙƙin ɗan-Adam da ƙasashen MƊD suka rattaɓa hannu kanta.

Mawallafi: Mösch/Tijani

Edita: Zainab Muhammed Abubakar