1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan somalia sun mika makamai

Zainab A MohammedJuly 13, 2006
https://p.dw.com/p/BtzB

sauran burbudin mayakan dake marawa shugabannin haulolin Somalia da Amurka ke marawa ba,wadanda kuma aka fatattakesu daga birnin Mogadisho,sun mika makamansu wa gamayyar kotunan islama a birnin Mogadisho a wannan rana ta alhamis.

Rundunar mayaka dake marawa shugabannin hauloli biyu baya,watau Bashir Raghe da Abdulkadir Bebe,sun mikawa wakilan gamayyar kotunan islama makaman fadansu a birnin mogadisho ayau,tare dayin alkawarin cewa a shirye suke su bada hadin kai wajen tabbatar da doka da oda a birnin Mogadisho dake zama fadar kasar ta somaliya.

Shugaban kotun sharia ta Al-Irshad,Sheikh Farah Ali Hussein ne ya bayyana karban makaman a yankin arewacin mogadisho,inda nan ne karban makaman ya gudana.

Bayan bukin karban makaman mayakan ne ya bayyana cewa wannan gagarumar nasara ce wa addinin islama da mogadisho dama alummar somaliyan baki daya.Yace godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki,daya kawo su wannan yanayi na samarwa kasar zaman lafiya.

Wannan bukin karban makaman mayakna dai yazo ne yini guda bayan da gamayyar kungiyoyin kotunan islaman sun karbe babbar tashar jiragen ruwa dake mogadisho,tare da sanar dacewa a mika musu dukkannin kaddarori mallakar gwamnatin somaliyan dake birnin Mogadisho,bayan gargadin da sukayi na cewa sabanin haka zai haifar da mummunan sakamako.ö

Tun a farkon wannan makon nedai mayakan kotunan Islaman suka zakulo dakarun dake marawa shugabbanin haulolin baya ,a wata arangama da sukayi na watanni da dama,fadan da aka kwantata shi dana yan Taliban a kasar Afganistan.

Kakakin Shirar,wanda ya taba mallakar arewacin birnin Mogadisho dai ya sanar dacewa,shugabannin haulolin baki daya sun ranta ana kare.bayan da aka ci galaba akansu.Omar Ali Adow,ya fadawa taron manema labaru cewa ,gamayyar kotunan yakin sun ci nasarar karbe birnin na Mogadisho,don haka yanzu hakki ya rataya a wuyansu,na samara da zaman lafiya.

Ya kara dacewa,idan suna bukatar tallafi,a shirye suke domin samarwa alummar somaliya zaman lafiya da kwanciyan hankali.

Nasaran da kungiyoyin gamayyar kotunan suka samu akan shugabannin haulolin dake zama yan koren Amurka,tun a ranar 5 ga watan Yuni dai,ya tayar da hakalin jamaa a dangane da shakkun samun zaman lafiya a wannan kasa data ddebi shekaru 16,cikin hargitsi da rigingimu.

Bugu da kari wadannan kotunan isklama dai na masu kasancewa barazana ce wa gwamnatin rikon kwarya dake da goyon bayan kasashen duniya,kuma ayanzu keda matsugunninta a garin Baidoa,dake yankin arewa maso yammacin birnin mogadisho.

A karshen makonnan nedai,wakilan kungiyoyin biyu zasu sake ganawa tsakaninsu,a birnin Khartun din Sudan,duk dacewa batun bukatun kotunan islaman na a mika musu kaddarorin gwamnati na barazana wa wannan sabon zagaye na sulhu.

Kungiyoyin Islan man dai sun sun karyata zargi da ake musu da alaka day an taadda.