Mayakan Kurdawa na kokarin kwace Rakka | Labarai | DW | 27.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayakan Kurdawa na kokarin kwace Rakka

Rahotanni daga kasar Siriya na nuni da cewa mayakan sa kai na Kurdawa tare da na Larabawa na ci gaba da samun galaba a kokarin da suke na kwato garin Rakka da ke zaman tungar 'yan IS.

Mayakan Kurdawa na kurdawa cikin garin Rakka

Mayakan Kurdawa na kurdawa cikin garin Rakka

A cewar kwamandan rundunar mayakan 'yan adawa na Syrian Democratic Forces SDF, kawo yanzu sun kwace kauyuka biyar da kuma wasu yankuna daga hannun IS din a garin na Rakka. Dakarun na SDF dai na taimakawa rundunar taron dangi da Amirka ke wa jagoranci a yakin na Siriya wajen yakar 'yan ta'addan na IS. Nasarar da mayakan na SDF ke samu a Rakka dai na zuwa ne kwana guda da fara kai hare-hare ta sama kan 'yan ta'addan IS din a birnin Fallujah da ke Iraqi.