1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Islama sun fice daga birnin Mogadishu

Mohammad Nasiru AwalDecember 28, 2006

To sai dai janyewar na matsayin sake dubarar yaki inji shugaban majalisar kotunan Islama Sheikh Ahmed.

https://p.dw.com/p/Btws
Sojojin sa kai a Mogadishu
Sojojin sa kai a MogadishuHoto: AP

Ba zato ba tsammani rikicin Somalia ya dauki sabon salo, bayan da mayakan kotunan Islama suka janye daga birnin Mogadishu. Shugaban majalisar kotunan Islama Sheikh Sharif Ahmed ya fadawa tashar telebijin ta Al-Jazeera cewa sojojin sa sun fice daga birnin, to amma an ji kararrakin amon manyan bindigogi a Mogadishu da sanyin safiyar yau. Tun kuwa a jiya dakarun Ethiopia suka danna zuwa wani yanki mai tazarar kilomita 30 daga Mogadishu, da nufin yiwa birnin kofar rago, inji jakadan Somalia a Ethiopia, Abdelkarim Farah.

“Mogadishu ce babban birnin Somalia, shi ya sa burin mu shi ne mu mayar da fadar gwamnati a can. To amma kamar yadda muka sani Mogadishun wata matsala ce ta daban.”

Bisa ga dukkan alamu wannan matsala ta kau bayan janyewar ba zata da ´yan Islaman suka yi. To sai dai suna gwamnatin wucin gadin ka iya fuskantar wasu matsaloli, domin ba wanda ya san inda sojojin Islaman suka dosa. Sannan shugaban su ya ce kawunan su a hade su ke kuma sun janye daga Mogadishu ne a wani mataki na sauyin dubarun yaki. Manazarta na ganin cewa sojojin sa kan zasu shiga yakin sunkuru ne a kasar ta Somalia.

To amma kakakin gwamnatin wucin gadi Abdirahman Dinari ya ce tuni an karya alkadarin shugabannin ´yan Islama, kuma yanzu haka sojojin gwamnati ne ke riko da muhimman hanyoyin shiga Mogadishu.

A kuma halin da ake ciki FM Somalia Ali Mohammed Gedi ya ce a yau zai gana da shugabannin garuruwan dake wajen Mogadishu kafin dakarun gwamnatin sa dake samun daurin gindin Ethiopia su shiga babban birnin. Ministan yada labaru Ali Ahmed Jama ya ce mista Gedi da tawagar sa za su tattauna da nufin tabbatar da dakarunsa sun shiga birnin Mogadishu cikin sauki.

Gwamnatin wucin gadin dai wadda aka kafa ta shekaru biyu da suka wuce, ba ta da wani tasiri a kasar. Wannan shi ne karon farko da zata sanya kafar ta a Mogadishu. Kuma ba´a sani ba ko birnin zai sake komawa karkashin ikon madugan hauloli. Su dai ´yan Islama sun fatattaki wadannan hauloli sannan kuma sun mayar da bin doka da oda a dukkan wuraren da suka kasance karkashin ikon su, kafin su fice daga Mogadishu, a wannan yanki da Amirka ta marawa Ethiopia baya, bisa fargabar cewa Somalia ka iya zama wata matattarar ´yan ta´adda na kasa da kasa.