Mayakan Al Shabab sun hallaka mutane a Somaliya | Labarai | DW | 08.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayakan Al Shabab sun hallaka mutane a Somaliya

'Yan tawayen Al Shabab sun kashe mutane a wani Otel a yankin Puntland na kasar Somaliya daf da zaben Shugaban kasa.

A yau ne 'yan majalisar kasar  Somalia za su kada kuri'a domin zaben shugaban kasa. Wannan zabe kuwa na zuwa ne daf da wani harin da mayakan Kungiyar Al Shabab suka kai a kan wani Otel da ke garin Bosasso na yankin Puntland inda suka hallaka masu gadi 4 yayin da mahara 2 kuma suka mutu.

Da safiyar Laraban nan ne dai maharan na Al Shabab suka farwa Otel din kamar yadda gwamnan yankin Yusuf Mohammad ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Maharan dai ba su shiga dakunan da ke a Otel din ba, sun buda wuta ne a ciki haraba kawai, lamarin da ya taimaka ba su kashe karin wasu bayan masu gadin ba. Gwamnan yankin na Bosasso ya kuma ce akwai wani daga cikin maharan da ya arce, sai dai a cewarsa ana nan ana bin sawun shi.