1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Al-Shabaab sun kai hari a Mogadishu

Salissou BoukariJune 25, 2016

A wannan Asabar mayakan kungiyar Al-Shabaab, suka kai hari a wani otel da ke Mogadishu babban birnin kasar Somaliya inda suka hallaka mtane da dama.

https://p.dw.com/p/1JDiF
Somalia Selbstmordanschlag auf Nasahablood Hotel in Mogadischu
Otel Nasahablood a MogadishuHoto: Reuters/F. Omar

Da farko dai maharan sun soma da jefa wasu ababe masu tarwatsewa, kafin daga bisani su buda wuta da bindigogi masu sarrafa kansu. Wani mutum mai suna Abdihafid Mudey, da ke kusa da otel din da ake kira Naasa Hablood, ya tabbatar cewa har ya zuwa wajejen karfe biyar na yamma ana ta harbe-harbe cikin otel din. Sai dai ba su san abun da ke faruwa ba, domin a daidai lokacin da yake sanar da kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP wannan labari, yana kwance ne a kasa domin tsira da rayuwarsa.

Wasu majiyoyi da dama na ma'aikatar tsaron kasar sun tabbatar da wannan hari, wanda kawo yanzu ya yi sanadiyyar rasuwar mutane akalla biyar cikinsu jami'an tsaro uku, tare da jikkata wasu mutane shida.