Mayaƙan Hamas sun ƙwace ragamar tsaro a Gaza | Labarai | DW | 15.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayaƙan Hamas sun ƙwace ragamar tsaro a Gaza

Mayakan sa kai na ƙungiyar Hamas sun karbe ragamar tsaro a ɗaukacin yankin zirin Gaza bayan da suka ƙwace alámuran tsaron gidan shugaban ƙasar Mahmoud Abbas. Wani mai magana da yawun Hamas Abu Obeida yace, a yanzu Hamas ce ke riƙe da dukkanin harkokin tsaro a yankin baki ɗaya ciki kuwa har da fadar shugaban ƙasa. Wannan hali dai ya raba kawunan Palasdinawa inda Hamas ke rike da yankin Gaza Fatah kuma ke iko a yankin gaɓar yamma. A halin da ake ciki dai shugaba Mahmoud Abbas ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasar, ya kuma sallami P/M Ismaila Haniya tare da kafa dokar ta ɓaci. Haniya ya baiyana matakin da Mahmoud Abbas ya ɗauka da cewa yayi gagawa kuma ba zai amince da dokar ba. A martanin Washinton, sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta kare matsayin da Abbas ɗin ya ɗauka tana mai jaddada goyon bayan Amurka a gare shi.