May: Muna bukatar hadin hadi kai da Amirka | Labarai | DW | 27.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

May: Muna bukatar hadin hadi kai da Amirka

Firaministar Birtaniya Theresa na zama shugaba ta farko daga wata kasa ta ketare da za ta gana da shugaban Amirka Donald Trump, ziyarar da ke zama zakaran gwajin dafi ga dangatakar Trump da kasashen Turai.

Firaministar Birtaniya Theresa May ta isa kasar Amirka domin ganawa da shugaba Donald Trump. Ziyarar da ke zama ta farko da shugaban na Amirka zai gana da wani shugaba na kasar waje.

Da ta ke jawabi ga taron shekara shekara na sanin makama kan manufofi na yan jam'Iyyar Republican a birnin Philadelphia, Theresa May ta nuni ga karkata akalar manufofinta na ketare tana mai baiyana matsayi daidai da na Trump.

Tana mai kira ga kasashensu biyu su hada kai domin tunkarar sabbin kalubale.

Ko da yake kasashen biyu na Amirka da Birtaniya su na da danganataka ta musamman a tsakanin su ziyarar na zama zakaran gwajin dafi a yadda manufar Trump z ata kasashe a danganataka da kasashen Turai.