Mawuyacin Halin Da Yara Ke Ciki A Sudan | Siyasa | DW | 29.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mawuyacin Halin Da Yara Ke Ciki A Sudan

A cikin wani rahoton da ya bayar a birnin Berlin a jiya litinin asusun taimakon yara na MDD UNICEF yayi nuni da yadda al'amuran rayuwa ke dada tabarbarewa, musamman dangane da yara kanana a kasar Sudan

An sha ji daga bakin jami’an siyasa cewar al’amuran rayuwa duk sun tabarbare a yammaci da kuma kudancin Sudan. A cikin wani rahoton da ya bayar a jiya litinin asusun taimakon yara na MDD UNICEF a takaice yayi bayani filla-filla a game da mawuyacin halin da yara ke ciki, inda ya ce dubban daruruwan yara ne ke cikin hali na rashin sanin tabbas game da makomar rayuwarsu. A lokacin da yake bayani Dietrich Garlichs daga reshen UNICEF dake Berlin karawa yayi da cewar:

Kimanin kashi 25% na yara ke mutuwa kafin su cika shekaru biyar na haifuwa a kasar Sudan. Yaran sun fi fuskantar barazanar mutuwa fiye da barazanar rashin samun wata dama ta halartar ajujuwan makarantu a can kudancin Sudan, lamarin dake bayani game da mawuyacin halin da jama’a ke ciki a kudanci da kuma yammacin kasar.

A yayinda ake hangen cimma wata yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnati da ‚yan tawaye a kudancin Sudan ta yadda za a samu kafar kai taimako ga wannan yanki, al’amura sai dada rincabewa suke yi a yammacin kasar, wacce tafi kowace girma a nahiyar Afurka. A halin yanzu haka mutane sama da miliyan daya ke kan hanyarsu ta gudun hijira a wannan yanki sakamakon barazanar kisan kiyashin da suke fuskanta daga dakarun sa kai Larabawa dake da daurin gindin gwamnati a cewar asusun na UNICEF. Ita ma karamar minista a ma’aikatar harkokin wajen Jamus Kerstin Müller wacce ta kai ziyarar yini biyar a yankin tayi tsokaci da mummunan halin da ake ciki a yammacin Sudan, inda aka yi fatali da wata yarjejeniya ta tsagaita wutar da aka cimma a watan afrilun da ya gabata. Bayan tattaunawar da tayi da shugaban kungiyar tarayyar Afurka Alpha Oumar Konare, karamar ministar ta sikankance cewar su kansu kasashen Afurka sun tashi haikan wajen tinkarar matsalar, kuma zasu samu cikakken goyan baya daga Jamus da sauran kasashen Turai in ji ta. Ta kara da cewar wajibi ne gwamnatin Sudan ta kwance damarar Larabawa ‚yan Janjaweed dake kai farmaki kan bakar fata a lardin Darfur. Muddin hakan ba ta samu ba to kuwa kungiyoyi na kasa da kasa zasu fara tunani akan matakin ladabtarwar da ya kamata a dauka kan kasar Sudan da kuma bin bahasi akan daidaikun jami’an kasar dake da alhakin wannan ta’asa ta keta hakkin dan-Adam. Jami’ar siyasar ta kara ta bayanin cewar mai yiwuwa ayi nazari akan haramta wa jami’an gwamnatin Sudan shigowa nahiyar Turai da kuma dora hannu akan kudaden ajiyar kasar a ketare. Ta bayyana farin cikinta a game da ziyarar sakatare-janar na MDD Kofi annan da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ga kasar ta Sudan a wannan makon. Wannan ka iya zama wani mataki na dada matsin lamba akan fadar mulki ta Khartoum.