1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

010910 Niedecken Engagement

September 1, 2010

Mawaƙin ƙungiyar makaɗa ta BAP dake birnin Kolon Wolfgang Niedencken ya daɗe yana fafutukar neman zaman lafiya a nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/P1nI
Wolfgang Niedecken na JamusHoto: AP


A ranar juma'a ne gaggan jami'an siyasa da 'yan kasuwa da na sauran ƙungiyoyin taimako masu zaman kansu zasu hallara a nan birnin Bonn domin su yi musayar miyau akan manufofin taimakon raya kasashe masu tasowa. Daga cikin mahalarta taron kuwa har da shahararren mawaƙin nan na zamani Wolfgang Niedecken, daga birnin Kolon, wanda babban burinsa shi ne a wayi gari duniya na cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kamanta adalci tsakanin dukkan 'yan Adam.

A wata waƙar da ya rera tare da ƙungiyarsa ta BAP Wolfgang Niedecken cewa yake yi: Da lamarin zai yi kyau da za a wayi gari ba wani mai fama da yunwa, ba wani da ake azabtarwa, ba mai rowa. Ba shakka da za a yi raba daidai da kuwa ba za a samu wani dalili na ta'addanci da hasada da kushe ba.

Akwai dai masu yi wa mawaƙin na ƙungiyar makaɗa ta BAP ba a a game da cewar kirkinsa na da yawa. Amma bai damu da ba'ar da ake masa ba. A wasu 'yan shekaru can baya Niedecken ya faɗa a cikin hira da wata jarida tayi da shi cewar:"Wai shin saboda wasu ba su ƙaunar matsayinsa a game da rashin adalcin da ake fama da shi a duniya sai ya shiga mugunta."

Kindersoldaten - Wolfgang Niedecken in Uganda
Wolfgang Niedecken tare da sojoji yara a UgandaHoto: picture-alliance/ dpa

Wolfgang Niedecken ya sha bayyana dalilinsa a game da ƙin watsi da matsalar tilasta wa yara aikin soja da ake yi da matsalar Uganda. Yayi wannan furucin ne a shekara ta 2004, lokacin da yayi balaguron Afirka tare da wasu 'yan jarida a matsayin wani jakadan Afirka. Ga dai bayanin da yayi

"Na jita a jika a arewacin ƙasar Uganda kuma hakan ta sanya na ce faufau ba zan dadara ba. A arewacin Uganda ne na fara ɗaukar wani tsayayyen matsayi. Kafin haka sai da na ziyarci Muzambik misalin shekaru 20 da suka wuce. Sai da na naƙalci yaƙin basasar ƙasar Muzambik, sannan a shekara ta 2004 da huɗu na tsayar da shawarar cewar ba zan fasa ba."

A wancan lokaci dai ana fama da yaƙin basasa a Uganda. A kuma wata cibiyar gyara hali ga tsaffin sojoji yara Niedecken ya sadu da wasu 'yan mata biyu, waɗanda aka sace su aka mayar da su bayi kuma suka sha fama da fyaɗe daga 'yan tawaye. Kuma bayan haka wani labari na baƙin ciki ya zo cewar dukkansu biyu da jariran da suka haifa suna da cutar Aids. Hakan ta sanya Niedecken ya rasa bakin magana a hirar da aka shirya zai gudanar da wata tawaga ta telebijin. A cikin wani bayanin da yayi Niedecken ya nuna manufar mayar da hankalinsa akan sojoji yara ƙanana a nahiyar Afirka:

"Mun gabatar da wani shiri a arewacin Uganda inda ake sake gina makarantun yankin da suka haɗa har da makwancin ɗalibai ta yadda yaran zasu iya kwana a can tsawon lokacin karantunsu a makarantun. A nan suna da ikon koyan wasu sana'o'i na hannu."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu