1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mauritania ta koka da karuwan bakin haure

Zainab A MohammadMarch 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7S

MURTANIA

Hukumomin kasar Muritania na kira ga kasashen duniya da hukumomin bada tallafi,dasu taimaka wajen shawo kann Dubban yan Afrika dake kokarin bita kasar akan haryarsu ta shiga turai.Tuni dai manyan jamian kasar Spain suka shiga kasar domin tallafawa shawo kann matsalar.A kowane dare dai akan samu ayarin matasa dake amfani da kanan kwale kwale dake bin cikin kogin Atlantika daga arewacin Muritania,wadanda ke fatan isa tsibiran Spain ,domin samun ayyukanyi domin su tallafawa iyalansu a gida.

To sai dai rahotanni daga kasar na nuni dacewa saboda irin wahala da sukan fada ayayin kutsawa ta wannan barauniyar hanye,dayawa daga cikinsu na rasa rayukansu.

Akan karuwar wannan mastsala ne Prime ministan Muritania Sidi Mohammed Ould Boubacar yayi kira ga kasashen duniya dasu kawo dauki,domin gwamnatinsa bata da sukunin hana wadannan bakin haure dake amfani da Murtania ,amatsayin hanya mafi dacewa na zuwa tsibiran na Spain.