1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsin tattalin arzikin Israila akan hukumar Palasdinawa

February 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7R

Hukumar gudanarwar Palasdinawa ta amince zata mayarwa da gwamnatin Amurka gudunmawar kudi dala miliyan 50 da Amurkan ta baiwa yankin Palasdinawa. Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas yace Amurka ta bukaci hukumar Palasdinawan ta maido mata da kudaden tun bayan da kungiyar Hamas ta sami rinjaye a zaben majalisun dokoki da aka gudanar. Mahmoud Abbas ya baiyana matsin harkokin kudade da Amurka da Israila suka yiwa hukumar Palasdinawan da cewa ya jefa ta cikin mawuyacin hali. Abbas yace bai kamata kasashen duniya su azabtar da alúmar Palasdinawa ba saboda zabin da suka yi bisa tafarkin dimokradiyya. Majalisar gudanarwar Israila ta zartar da dakatar da baiwa hukumar Palasdinawa kudaden haraji na wata wata da take karba a madadin hukumar Palasdinawa na kayayyakin da ake shiga da su yankin Palasdinawa. Kudaden wadanda suka kai dala miliyan 50 a kowane wata, Israila ta ce ba zata bayar da su ga hukumar Palasdinawan ba, domin kada su fada hannun Hamas.