Matsayin Sin a Rikicin Myanmar | Zamantakewa | DW | 27.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsayin Sin a Rikicin Myanmar

Irin rawa da kasar sin ke takawa a Rikicin democradiyyar Myanmar

Rikicin Myanmar

Rikicin Myanmar

A yanyinda kasar Burma ko kuma Myanmar ke cigaba da fuskanatar rigingimu na muradin Democradiyya a bangaren alummomin wannan kasa,gwamnatin soji a daya hannun na kokarin ganin cewa ta kawo karshen wannan rikici ta kowane hali.Ayayinda kasashen duniya ke marawa wannan yunkuri na neman Democradiyya a kasar ta Burma,a hannu guda kuma akwai kasashe da kamar Sin da Indien dake da hannu a wannan riciki,saboda irin goyon baya da suke dashi wa gwamnatin sojin.

Halin da ake ciki a Myanmar dai ya kasance batu na damuwa a bangaren kasashen duniya ,musamman a dangane da irin rayuka da ake cigaba da yin asaran su sakamakon wannan rikici na muradin democradiyya daya barke a wannan kasa.Duukkan Kasashen yammaci na turai da ma mdd na cigaba da kira adangane da daukar matakai da suka dace na kawo karshen halin da kasar take ciki a yanzu.

To sai dai bisa dukkan alamu ayayinda mafi yawa daga kasashen duniya ke lalubaen bakin zaren warware halin da ake ciki a Mayanmar din,akwai wasu kasashe da ke da hannu a irin badakkalar da gwamnatin sojin ke tafkawa a wannan kasa.Marco Bünte,dake zama kwararre kann lamuran kasar ta Burma a cibiyar nazarin harkokin yankin Asia dake birnin Hamburg anan jamus yayi bayanin ummul abaisin wannan takaddama…

„Myanmar tana da dangantakar cinikayya a la misali coiki da ta yammaci da Amurka alal misali .Saannan kasashen duniya baki daya na muradin ganin an kara mata takunkumi,daura da wanda aka dora mata a baya,wanda suka hadar da takunkumin cinikin makamai da tallafi daga hukumomin bada agaji ,alal misali babban bankin duniya.Gwamnatin kasar bata da hulda daga ketare sai dai da manyan kasahen yankin Asia,watau Sin da India,kuma kasancewar wadannan sune jigon kasashen nahiyar.Sai kasar Sin tun a baya ta tsoma hannun ta dumu dumu cikin harkion Myanmar,kuma yanzu zata iya taimakawa wajen kawo karshen wannan Rikici“

Wasu yan adawan kasar ta Burma dake gudun hijira a ketare dai suna masu raayin cewa duk da matsayin kasar ta Sin a wannan kasa,hankalin ya koma ne kann awsu batutuwan da suka shafe ta a maimakon ta taimaka wajen warware matsalar.,kamar yadda wani dan kasar ta Myanmar dake gudun hijira a Thailand ya shaidar…

„Kasar ta Sin wadda ke marawa gwamnatin sojin baya,ta dukufa ne a yanzu wajen shirye shiryen wasannin motsa jiki na Olympics da zata zama mai masaukin baki a shekarata 2008 mai gabataowa,Kuma a yanzu haka akwai matsin lamba daga kasashen duniya ,adangane da goyon baya a wannan fafutuka na tabbatar da tafarkin democradiyya a.Kowa na muradin ganin cewar kasar ta Burma ta koma tafarkin democradiyya ,dalili kenan daya sa sojojin ke cigaba da kashe mutane,basu da da halin da ake ciki ba,amma gwamnatin tana darajawa kasar ta Sin“

Yan adawan kasar ta Mayanmar dai na fatan cewa kasar ta Sin zatayi amfani da wannan danganrtaka dake tsakaninta da gwamnatin sojin,wajen ganin cewa an gano bakin zaren warware wadannan rigingimu da kasar ke fama dasu ba tare da cigaban zubar da jini ba.

Marco Bünte a daya hannun na ganin cewa rikici a kasa guda ,zaa iya cewa rikici ne da zai iya shafar yankin baki daya,adangane da hakane ya kamat Sin ta kasance cikin shirin kota kwana…

„Kada a mace cewar kasashen dake yankin na hada kann iyakoki,abunda ke nufin cewa dukkan halin kunci da alummomin kasar Mayanmar suka fada ,zai yi tasiri a sauran kasashen dake wannan yankin,wanda kazalika zai hadar da ita kanta Sin,ta tuna cewear idan ta taimakawa samar da zaman lafiya a Mayanmar tayiwa wannan yanki ne baki daya.