Matsayin Sabiya game da ′yancin kan Kosovo | Labarai | DW | 23.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsayin Sabiya game da 'yancin kan Kosovo

ƙasar Sabiya ta ƙi bayar da kai ga hukuncin kotun duniya game da 'yancin kan Kosovo.

default

ƙasar Sabiya ta lashi takobin ci gaba da aiwatar da manufofinta a Kosovo duk da hukuncin da kotun ƙasa da ƙasa ta yanke game da taƙaddamar 'yanci da ke tsakaninsu. Ita kotun ta Majalisar Ɗinkin Duniya da cibiyarta ke birnin The Hague ta ƙasar olland, ta ce ayyana kanta a matsayin ƙasa 'yantata da Kosovo ta yi bai saɓa ma dokokin ƙasa da ƙasa ba. Sai dai Sabiya ta ce za ta ci gaba da ɗaukar Kosovo a matsayin wani lardinta da ke neman ɓallewa. Dama ba wajibi ba ne ƙasashe biyu su yi aiki da hukuncin da ta kotun ta yanke. 

Amma kantomar harkokin wajen EU wato Catherine Ashton ta ce ƙungiyar gamayyar ta Turai a shirye take ta shiga tsakanin ƙasashen biyu, domin warware taƙaddamar ta hanyoyin dipolomasiya. Ya zuwa yanzu dai, ƙasashe 69 ne cikin duniya suka amince da 'yancin kan ƙosovo, ciki kuwa har da Amirka da kuma ƙasashe 22 da ke da kujera a Ƙungiyar Tarayyar Turai.Yayin da a ɗaya hannun, ƙasashen Sabiya da kuma Rasha ke ci gaba da fatali da batun na 'yancin Kosovo.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou