1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

210312 Russland Syrien

March 21, 2012

Rasha ta amince ta ba da hadin kai ga shiga tsakanin Kofi Annan a rikicin Siriya.

https://p.dw.com/p/14OY5
Syrian President Bashar Assad, right, meets with Russian Foreign Minister Sergey Lavrov in Damascus, Syria on Tuesday, Feb. 7, 2012. Syrian forces renewed their assault on the flashpoint city of Homs on Tuesday as Russia's foreign minister held talks in Damascus with President Bashar Assad about the country's escalating violence. (AP Photo, pool)
Assad da Sergei LavrovHoto: AP

Mun amince da ƙuduri kan ƙasar Siriya amma idan fa idan ƙudurin da Kofi Annan ya bayar ne, wanda ya buƙaci dukkan ɓangarorin dake yaƙar juna, wannan shine jawabin ƙasar Rasha a kan rikicin Siriya. Don haka sassau towar ƙasar Rasha a kan rikincin Siriya babu tabbas.

Ministan harkokin wajen Rasha Sargei Lavrove ya yi wani jawabin da ake ganin kamar na sassautowar ƙasar ne kan matsayin ta rikicin Siriya. Wata ƙila dalilan hakan shine rahoton da wakili MDD da ƙasashen Larabawa kan rikicin Siriya wato Kofi Annan ya bayar, kana yadda al'amuran Siriya ke ƙara rin caɓewa fiye da da.

Mun yaba da matakan, idan zasu taimakawa ƙawayenmu. ma'ana mun a cewa mun sauya matsayinmu. Da sunan Allah, Babbar buƙatarmu shine, war-ware rikicin

Batun sauyin ra'ayi daga ɓangaren ƙasar Rasha a rikicin Siriya ba wani abune da za'a iya yin magana a kai ba. Domin ƙasar Rasha zata ci gaba da hana duk wani mataki Majalisar Dinkin Duniya, muddin dai zai ci gaba da yin bazarabna ga gwamnatin Siriya. A ra'ayin ƙasar Rasha bazata taɓa amincewa a zargin ɓangare guda, alhali kowa na da laifi arikicin. Kana ƙasar Rasha zata ci gaba toshe duk wata ƙafar matakin sojin ƙasashen waje a Siriya.

A view of the Security Council as Vitaly I. Churkin, Permanent Representative of the Russian Federation to the UN, on behalf of his Government, vetoes a draft resolution strongly condemning the violence perpetrated by Syrian authorities against civilian protesters. The draft resolution was also vetoed by China, received nine votes in favour and four abstentions. Photo: United Nations/ Paulo Filgueiras +++(c) dpa - Bildfunk+++
Taron UN game da SiriyaHoto: picture-alliance/dpa

Mafi ƙaranci akwai matakai biyu da zamu amince da su, na ɗaya shawar da Kofi Annan ya bayar dole batsa ayi wata rufa-rufa akanta ba. Na biyu duk ƙudurin kwamitin sulhu dole bazai ƙumshi barazana kan gwamnatin Siriya ba. Dule abi matakin sannu a hankali. Shawar Kofi Annan dole ta zama shimfiɗa ga yan ƙasar Siriya, wato, ɓangaren gwamnati da yan tawaye"

Sai dai ƙasar Rasha ta amince da shawar Kofi Annan tacewa cewa a bude ƙofa don kai agajin gaggawa ga ma buƙata. Ta yadda dukka masu ɗauke da makamai zasu tsagaita wuta. kana a fara tattaunawar siyasa.

Ministan harkokin wajen Rashan ya kuma ce dole ƙasashen maƙobta dake baiwa yan tawaye makamai su daina. Domin kuwa waɗannan ƙasashe n dake baiwa yan tawaye makamai suna ƙara dagula al'amuran ne kawai a Siriya.

Syrian President Bashar al-Assad receive U.N. Secretary General, Kofi Annan Friday Sept. 1, 2006 in Damascus. The Secretary-General said Friday that Syria would step up border patrols and work with the Lebanese army to stop the flow of weapons to Hezbollah. During the meeting Annan also asked Syria to "use its influence" to help win the release of three Israeli soldiers held by Lebanese and Palestinian militants allied with Damascus. (AP Photo/Sana)
Ziyarar Kofi Annan a SiriyaHoto: AP

Ina magana bawai ga yan ta'adda dake kai hare-haren bama-bamai, wadanda suka kai hari a biranen Damskus da Aleppo a yan kwanakin nan. Wannan Wannan wata babbar tsokana ce, wanda kuma shine abinda Kofi Annan yake son kawar da shi. Abba abinda ke ƙara kawo koma baya shine, janye jakadun ƙasashe Larabawa daga Damaskus, da kuma ƙarin takunkumin ƙasashen EU kan gwamnatin Siriya, da kuma guna gunin da ake yi kan jiragen yaƙin ruwa na Rasha dake gaɓar ƙasar Siriya.

Ministan na harkokin wajen Rasha ya buƙaci da ƙara baiwa Kofi Annan daman shiga tsakani, a dai dai lokacin da ake jiran Kofi Annan din ya kai ziyra Moscow don tattauna rikicin na Siriya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi