1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Myanmar a tsakanin kasashen Gabashin Asia

Zainab MohammedNovember 21, 2007

Kokarin Majalisar Dunkin Duniya a Myanmar

https://p.dw.com/p/CQ8i
Taron Shugabannin gabashin AsiaHoto: AP

Jakadan Majalisar Ɗunkin Duniya na musamman zuwa ƙasar Myanmar,Ibrahim Gambari yayi imanin cewar ƙokarinsu zai yi tasiri da haɗin kan kasashen yankin gabashin Asia da sauran ƙasashe.

“Ibarahim Gambari yace hukumomin Myanmar sun bayyana min cewar a shirye suke su bada haɗin kai da Majalisar Ɗunkin Duniya ,yanzu haka zamuyi gwajin wannan Alkawari da suka yi.Amma a tattaunawa da nayi da Prime ministan kasar,ya tabbatar min da manufar gwamnatinsa na aiki tare da Majalisar,kumaa mun taɓo batun sake komawa ta Myanmar,wanda nake fatan nan bada jimawa ba”.

Kokarin da akayi daga ɓangarori daban-daban,da suka haɗar da ɗaukar matakai na ladabtarwa a ɓangaren kungiyar tarayyar turai EU dai,sun gaza cimma bukata da akeyi na bukatar gwamnatin mulkin sojin Myanmar din,ta gaggauta mayar da kasar karkashin mulkin Democraɗiyya ta hanyar yin gyare-gyare.

Gambari wanda yake ke ƙasar Singapore,domin bayani wa shugabannin gwamnatocin ƙasashe 16 dake halartan taron kasashen yankin gabashin Asia, adangane da cigaba ko kuma akasin da aka samu adangane da halin da ake ciki a Myanmar,ya gaza yin hakan sakamakon adawan da Myanmar ɗin tayi.

Adangane da haka ne ministan harkokin waje na ƙasar Australia Alexander Downer yace..”Ina takaicin cewar,Prof.Gambari ya kasa bayanin tattaunawar da yayi da magabatan Myanmar.alokacin daya ziyarci ƙasar,dangane da irin cigaba ko kuma akasi haka”

A maimakon jawabi wa taron shugabannin dai,Jakada Gambari ya gana a lokuta daban-daban da shugabannin dake halartan taron nqa Singapore,waɗanda suka haɗar da prime minister Thein Sein na Myanmar da ministan harkokin ketare Nyan Win.

Sai dai yace suna muradin Democraɗiyya zaunanniya a Myanmar ,kuma zasu aike da sakon daya dace alokacin daya kamata.”Gambari yace idan alal misali tattaunawar an fara ta,majalisar ɗunkin duniya nada muhimmiyyar rawa da zata taka a matsayin mai shiga tsakani,kuma dole ne mu kasance cikin shiri na bada shawarwari”.

Prime ministan Singapore Lee Hsien Loong,wanda ya ɗauki nauyin ziyarar ta Ibrahim Gambari ,yace Myanmar ta zame musu ƙashin wuya wanda dole ne su ɗauki mataki na ladabtar da ita.

A matsayin Singapore na shugabar ƙungiyar ƙasashen dake yankin kudu maso gabashin Asia na yanzu,Lee yace babu ɗaya daga cikin wakilan ta,dake goyon bayan sanyawa Myanmar takunkumi.