Matsayin MDD a game da rikicin Ethiopia da Erythrea | Labarai | DW | 08.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsayin MDD a game da rikicin Ethiopia da Erythrea

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Ban Ki Moon, ya gabatar da rahoto, a game da halin da ake ciki, a rikici tsakanin Ethiopia da Erythrea.

Ban Ki Moon, ya ce, ya na tare da zullumi, ta la´akari da ƙara taɓarɓarewa mu´amila, tsakanin ƙasashen 2 ,duk da yarjeniyar zaman lahia da su ka cimma.

Dangantaka tsakanin Ethiopia da Erythrea, ta ƙara gurbacewa, a sakamakon rikicin ƙasar Somalia.

Ethiopia, ta yi kaka gida a Somalia, ta hanyar bada gudumuwa ga sojojin gwamnati, a yayin da Ethyrea, ƙarara, ta bayyana kai tallafi ga dakarun kotunan Islama.

Wannan hali a cewar Ban Ki Moon, na ɗauke da babbar barazana ga zaman lahia a yankin ƙafon Afrika baki ɗaya.

A game da rikicin iyakoki tsakanin maƙwabtan 2, sakatare Janar an Majalisar Ɗinkin Dunia, ya yi kira ga Ethiopia, ta mutunta hukunci da wani komitin ƙasa da ƙasa mai zaman kansa ya yanke a shekara ta 2002.

Sannan ya bukaci Erythrea, ta janye takunkumin da ta sakawa tawagogin Majalisar Ɗinkin Dunia, a wannan yanki.