1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Faransa game da ƙabilar Roma

September 17, 2010

Shugaban Faransa ya ce babu gudu babu ja da maya a yunƙurinsa na korar 'yan ƙabilar Roma daga ƙasarsa.

https://p.dw.com/p/PEIT
Shugaba Nicolas sarkozyHoto: AP

Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da aiwatar da manufarsa ta korar 'yan ƙabilar Roma daga ƙasarsa. A lokacin da ya yi jawabi a taron ƙolin shugabannin EU da ya gudana a birnin Brassels na ƙasar Beljium, Sarkozy ya nunar cewa matakin da gwamantinsa ta ɗauka na fatattakar 'yan rabbana ka wadata Romaniya i zuwa ƙasarsa ta asali ba ta saɓawa dokokin Turai ba, ya na mai cewa tarayyar Jamus ma na shirin ɗaukan mataki makamancin wanda ƙasarsa ta ɗauka. sai dai shugabar gwamantin Jamus wato Angela Merkel ta ƙaryata wannan furuci na Sarkozy.

Danganta korar 'yan ƙabilar Roma da Faransa ke yi da tasa ƙeyar yahudawa i zuwa sansanonin gwale gwale da komishiniyar EU mai kula da harkokin shari'a wato Viviane Reding ta yi ne- ya ke ci wa Sarkozy tuwo a ƙwarya. Duk da cewa daga bisa komishiniyar ta janye kalaman nata, amma kuma Sarkozy ya ce Viviane Reding ta ci mutunci ƙasarsa. Shugaban na Faransa wato Nicolas Sarkozy yayi misayar zafafan kalamai da shugaban hukumar zartaswa ta EU wato Jose Manuel Baroso dangane da wannan batu na korar 'yan ƙabilar Roma.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou