MATSALOLIN YIN HIJIRA TA NEMAN RAYUWA MAI ARMASHI | Siyasa | DW | 03.02.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MATSALOLIN YIN HIJIRA TA NEMAN RAYUWA MAI ARMASHI

A yanzu haka babban batun daya fi daukar hankali ake kuma kace nace a kansa a kasar Africa ta kudu shine irin yadda mutanen kasar bakake da farare masana a fannonin ilimi daban daban suke ficewa daga kasar izuwa wasu kasashe na ketare don neman guraren aiki da sukafi nasu nada.
A yanzu haka an tabbatar da cewa da dama daga cikin yan kasar wadanda suka shahara a fannin aikin likita da koyarwa da kuma aikin inji mai kwakwalwa ne ke ficewa daga kasar izuwa wasu kasashe da suka hada da Amurka da Biritaniya da New Zealand da Holland da kuma Australia.
An dai kiyasta cewa mutanen kasar ire iren wadanda muka lasafta a baya kusan dubu goma sha daya da dari shida da saba,in da daya ne sukayi kaura daga kasar a shekara ta 2003 data gabata.
A kuwa ta bakin shugaban wani kamfani mai zaman kansa a kasar ta Africa ta kudu mai suna Mr Brian Khumalo,a yanzu haka a kowace shekara sai bakake masana yan kasar sun fice izuwa wasu kasashe na ketare don samun aiki mai gwabi gwabi da zai basu hurumin more rayuwar su yadda suke bukata.
Babban dai dalilin ficewar wadan nan masanan na kasar ta Africa ta kudu izuwa wasu kasashe shine na karacin albashin da ake basu a kowa ne wata wanda da dama daga cikin su sukace yayi musu kadan bisa yadda zasu tafiyar da rayuwar su data iyalansu a kasar yadda suke so.
Wamn nan matsala a yanzu haka ta haifar da babbar matsala a kasar na karancin masana a fannoni daban daban na rayuwa,wanda hakan yayi sular gudanar da tarurruka na tattauna hanyoyin daya kamata a dauka don shawo kann al,amarin tun kafin ya shige gona da iri. A hannu daya kuma wani babban abin bakin ciki a cewar babban daraktan hukumar bincike ta kasar,Micheal Kahn shine a duk sailin da mutanen sukazo ficewa daga kasar sai suce zasu tafi aiki ne na tsawon shekara daya ko kuma biyu su dawo,amma idan sun tafi ko duriyar su baza a sake jiba.
Ita kuwa hukumar kwadago ta kasar ta hanyar shugabanta, Wiliam Madisa,a yanzu haka kasar ta Africa ta kudu ta fada cikin wani hali na kaka ni kayi sakamakon rashin kwararru da masana da take fama dashi a fannoni daban daban na rayuwar bil adama.
Bisa kuwa rahotannin da suka iso mana ba kawai kasar Africa ta kudu ce fuskantar wannnan matsala ba,da dama daga cikin kasashen nahiyar Africa na cikin matsalar tsundum.
A misali mataimakin shugaban Jamiar kasar Ghana Edward Ofori,a shekarar data gabata a can birnin accra ya fadi cewa a kowace shekara ta Allah ta,ala sai kwararru yan kasashen Nahiyar Africa dubu 70 sun fice daga nahiyar izuwa wasu kasashe na ketare don neman tagomashi.
Ita kuwa hukumar kula da tattalin arziki ta kasar habasha cewa tayi a tun shekara ta 1980 nahiyar africa ta rasa rabin masanan ta da kuma kwararru da take dasu a fannoni daban danan na rayuwar bil adama sakamakon ficewa da suke izuwa kasashen ketare.
Bugu da kari a cewar ofishin kula da baki na kasar Amurka a yanzu haka akwai yan kasar Nigeria dubu 250 dake zaune a kasar suna aiki iri daban daban.
Idan kuwa ana son a juyo da wan nan mataki izuwa daidai to ya zama wajibi a canja taka rawa ta yadda rawar zata zamo abin so abin karba ga mutanen nahiyar,wanda hakan zai basu damar zama a cikin kasashen nasu su kuma yi aikin da ake da bukata.