Matsalolin ′yan usulin Afurka a Jamus | Siyasa | DW | 26.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalolin 'yan usulin Afurka a Jamus

Akasarin 'yan Afurka dake zama na kaka-gida a nan kasar ta Jamus su kan sha fama da matsaloli a dangantakarsu da takwarorinsu Jamusawa a saboda dalilai iri dabam-dabam abin da ya hada har da jahilcin dake tattare da Jamusawan a game da al'amuran Afurka

Akasarin Jamusawa ba su da wata masaniya a game da nahiyar Afurka, wacce a ganinsu ba ta da wata kyakkyawar makoma ta la’akari da ire-iren rahotannin da kafofin yada labarai kan gabatar dangane da wannan nahiya. Duka-duka abin da Jamusawan suka sani dangane da Afurka shi ne kasancewarta nahiyat mai fama da talauci da yake-yake na basasa da bala'o'i’ daga Indallahi kamar yadda aka ji daga bakin Joseph McIntyre, mai koyarwa a jami’ar Hamburg, wanda kuma ya kara da cewar:

Tarihin bakar fata a nahiyar Turai ya saba da na sauran al’uma. Domin kuwa an tilasta musu aikin bauta kamar dai su din ba cikakkun ‚yan-Adam ba ne. Kuma ko da yake launin fata da tarihi na taka muhimmiyar rawa, amma babban abin dake hana ruwa gudu wajen hulda da ‚yan usulin Afurka shi ne jahilci na Turawa a game da al’amuran wannan nahiya.

Wannan jahilcin kuwa yana mummunan tasiri ga rayuwar bakar fata, musamman a nan Turai, inda da zarar an yi batu a game da cinikin miyagun kwayoyi zaka ga mahukunta na tuhumar dukkan bakar fata dake nan kasar, alhali kuwa duka-duka yawan bakar fata dake da hannu a wannan danyyen aiki bai zarce kashi biyar cikin dari ba. Bakar fata kan sha fama da wahala a kasuwar kodago, inda zaka tarar da kwararren ma’aikaci ya kama wani aikin da bai cancanci matsayinsa ba saboda launin fatarsa kawai. Kuma ko da yake matsaloli na talauci shi ne kan iza keyar bakar fatar Afurka yin kaura zuwa kasashen Turai, amma babban abin dake taka rawa wajen bin wannan manufa shi ne rashin hangen wata kyakkyawar makoma ga rayuwarsu. Kazalika, ko da yake akasarin bakar fatar kan koma gida bayan tsumulmular kudi na tsawon shekaru da dama ta yadda zasu samu wata madogara ta rayuwa a gida, amma akwai wasu da kan ci gaba da zama a nan kasar tare da kokarin cude-ni-in-cude-ka da takwarorinsu Jamusawa. To sai dai kuma galibi murnarsu ta kan koma ciki saboda rashin haba-haba da su da kuma nuna musu kyama da ake yi, kamar yadda aka ji daga Ahmad Samake daga Nijeriya dake nazari a jami’ar Hamburg, inda yake cewar:

Sau tari ni kan yi zama na ne a gida ina kallon telebijin ko kuma abota da sauran baki daga kasashen ketare. Amma dangane da Jamusawa ba ni da aboki Bajamushe ko da kwaya daya. Wato dai a takaice, bayan shekaru hudu da zama a Hamburg, har yau ji nike kamar a jiya ne na iso nan kasar.