1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin 'yan jarida a Afurka

May 2, 2005

'Yan jarida 15 daga sassan Afurka dabam-dabam ke neman mafaka a wani gidan da aka tanadar musu a Paris, fadar mulkin kasar Faransa

https://p.dw.com/p/BvcD

‚Yan jaridar dake neman mafaka a kasar Faransa, an tanadar musu da wani gida ne, mai fadin murabba’in mita 850 a kudu-maso-yammacin birnin Paris, fadar mulkin kasar. A halin yanzu haka ‚yan jarida 15 daga sassa dabam-dabam na nahiyar Afurka ne ke zaune a wannan gida, inda ake karbar bakuncinsu har tsawon watanni shida. A tsakaninsu akwai wani da ake kira Dauda mai shekaru 30 da haifuwa daga kasar Mauritaniya. A hannunsa akwai wani babban tabo na kunar wuta, sakamakon azabtarwar da ya sha fama da ita lokacin da aka tsare shi a gidan wakafi sakamakon wani rahoton da ya bayar a cikin wata majalla ta tarbiyya a kasar ta yammacin Afurka. Ya ce ya sha rubuta rahotanni dabam-dabam, musamman dangane auren mata ‚yan kanana da bas u cika shekaru na balaga ba. A lokacin da ya gabatar da irin wannan rahoto, wani babban malami na kasar ya ji tamkar hannunka mai sanda ne ake masa, a sakamakon haka ya ba da umarnin da a tsare shi tare da babban editan mujallar. Bincike da dan jaridar mai suna Daouda yayi ya gano cewar malamin na da wata mata ‚yar shekaru takwas kacal da haifuwa kuma tuni yake saduwa da ita. A maimakon mahukunta su bi bahasin gaskiyar lamarin sai aka zargi dan jaridar da kokarin bata sunan wannan malami. Bisa ga ra’ayin Douda dai wannan wata manufa ce ta cin mutuncin musulmi baki daya. Ita dai kasar Mauritaniya, ba abin dake ci mata tuwo a kwarya a game da ‚yancin ‚yan jarida. A cikin jerin kasashe 167 da kungiyar Reporteurs sans frontiers ta lissafta Mauritaniya ce ta 138 tsakanin kasashen da basa ganin hurumin ‚yan jarida. Ita kuwa kasar Sengela ko da yake ita ce ta 80, amma tilas ne mutum yayi sara tare da duban bakin gatarinsa wajen gabatar da rahotanni, musamman wadanda ke sukan manufofin gwamnati, in ji wani dan jaridar kasar da ya canza sunansa zuwa Abdoulaye, saboda ya kare lafiyarsa. A sakamakon rahotannin da yake rubutawa a game da tawayen ‚yan kudancin kasar, gwamnati ta zarge shi da yunkurin ba wa ‚yan tawayen dake neman ballewa daga kasar ta Senegal goyan baya. Sai dai kuma duk da barazanar da aka sha yi masa, amma ba a taba kai farmaki kann Abduolaye ba, bisa sabanin sauran takwarorinsa. Ya ce mai yiwuwa a saboda ya tsere daga kasar ta senegal akan lokaci ne. Kafofin yada labaran Faransa da Kungiyar Tarayyar Turai ne ke daukar nauyin ‚yan jaridar da suka yi kaura daga kasashensu sakamakon farautarsu da mahukunta ke yi. Tuni kungiyar ta tarayyar Turai ta ware wasu kudaden domin bude irin wannan gida na karbar bakuncin ‚yan jaridan dake fuskantar muzantawa a kasashensu, a birnin Berlin, fadar mulkin Jamus.