1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin 'Yan gudun Hijira

Ahmad Tijani LawalDecember 18, 2007

'Yan Afirka dake gudun hijira ta Maroko

https://p.dw.com/p/CdLO
TekuHoto: Steffen Leidel

An kiyasce cewar kimanin ‘yan gudun hijirar Afurka dubu goma zuwa dubu 30 suka tagayyara a kasar Maroko. Ko da yake ana hakuri da zamansu a kasar amma ba wani mai daukar alhakin kula da makomarsu duk da cewar tun a shekara ta 1990 ne aka cimma yarjejeniyar Geneva dake kare hakkin ‘yan gudun hijirar dake barin kasashensu don ci rani a ketare. Wani abin lura dai shi ne kasar Maroko bata rattaba hannu kan wannan yarjejeniya ba daidai da sauran kasashen Turai, lamarin dake ma’anar cewa ‘yan gudun hijirar suna kasar ta Maroko ne kara zube ba su da wani ‘yanci na kare hakkinsu. Wani da ake Paul daga kasar Kongo dake da shekaru 26 na haifuwa ya gabatar da takardunsa na neman mafakar siyasa a kasar Maroko tun misalin shekaru biyu da suka wuce tare da yin rajista a ofishin kungiyar ‘yan gudun hijira ta MDD UNHCR a takaice, amma an yi fatali da takardun nasa daga bisanin nan kuma ta haka yayi asarar takardar shaida kwaya daya dake tare da shi.

“Sun yi fatali da ni suka kuma bar ni ba tare da takardun shaida ba. A yanzun in na shiga matsala wa zan tuntuba? Sun kwace takarduna sannan suka ce a yanzun bani da wani iko na neman mafakar siyasa. Su kuwa ma’aikatan kungiyar ‘yan gudun hijira ta MDD juya mini baya suka yi suka ce da ni wai iya ruwa fid da kai. A yanzun ina cikin wani hali ne na kaka-nika-yi.”

Paul dai yana cikin rudami da rashin sanin tabbas saboda ba ya da wata takardar shaida da zai iya gabatarwa ga mahukuntan Maroko. Baya da fasfo, baya da izinin zama kuma ba shi da wani abin dake nuna cewar shi dan gudun hijira ne. A takaice baya da wata kariya ta doka. Wannan kaddarar da ta rutsa da Paul ita ce ‘yan Afurka kimanin dubu 10 zuwa dubu 30 ke fama da ita a Maroko, inda suke fuskantar muzantawa daga mahukuntan kasar. An saurara daga Chadi Sidhom dan kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Euromed yana mai cewar:

“A hakika a kasar Maroko dan gudun hijira ko dan ci rani ba ya da wata kariya ta doka, duk kuwa da cewar ita kanta kasar ta Maroko na da hannu a yarjejeniyar ‘yan gudun hijira kuma kungiyar ‘yan gudun hijira ta MDD ta dade tana gudanar da ayyukanta a kasar.”

Ita yarjejeniyar ta ‘yan gudun hijira ta MDD dai a shekara ta 1951 aka gabatar da ita kuma Maroko ta sanya hannu kanta a shekara ta 1956, amma bata biyayya da kudurorinta sau da kafa. A shekara ta 2005 sai da mahukuntan Maroko suka halaka ‘yan gudun hijirar Afurka masu tarin yawa a lokacin da suke kokarin tsallakowa zuwa Turai A sakamakon haka ‘yan gudun hijirar ke cikin fargaba a kodayaushe, in ji Chadi Sidhom, ya kuma kara da cewar:

“Suna rayuwa ne a cikin tsoro game da farauta da kuma muzanta musu. Hatta bakin haure, wajibi ne a ba su kariya, amma ba a rika azabtar da su ba. Dukkan wadannan abubuwa na kunshe a yarjejeniyar ta Geneva da kasashen Turai da Maroko ke da hannu a cikinta.”