1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalolin rayuwa ga sojoji bayan yaƙi

Sojojin da ke shaida mutuwar abokan aikinsu a harin da abokan gaba ke kai kansu, suna ɗaukar lokaci mai tsawo suna juyayin wannan al´amari

default

Sojan Jamus a Kundus, Afganistan

Sau da yawa sojojin da ke shaida mutuwar abokan aikinsu a harin da abokan gaba suka kai kansu, suna ɗaukar lokaci mai tsawo ba su manta da wannan abu ba bayan sun koma gida daga fagen daga. Hakan na zama wata damuwa mai tsanani da wani lokacin ya kan zame musu tamkar taɓin hankali, kamar yadda wasu sojojin Jamus da suka dawo gida daga Afganistan suke fama da shi.

Dirk Preusse likita ne dake kula da sojoji a asibitin rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr dake birnin Koblenz ya bayyana irin mawuyacin hali da tsananin damuwa da wasu sojojin ƙasar da suka dawo gida daga Afganistan su kan yi fama da shi lokaci mai tsawo. Munanan abubuwan da suke gani a fagen daga ya kan daɗe a cikin tunaninsu ba su mantawa da shi ba, wani lokaci ma yana firgitarsu kuma yana hana su barci sannan da sun ji ƙarar wani abu ko a cikin gida ne sai su razana. Abin da ke janyo haka kamar yadda Dirk Preusse ya nunar shi ne sojojin ba sa samun isasshen lokaci a fagen daga don sake tunanin abubuwan dake wakana, sai bayan sun dawo gida sun koma cikin hayyacinsu sannan suke tunawa da abin da ya faru a baya.

"Kusan ko-wanne daga cikinsu yana fama da wannan mawuyacin halin na tunawa da munanan abubuwan da suka faru a fagen daga. Kowa da abin da yake gani ko ji dake tuna masa abin da ya faru a baya. Alal misali ga sojojinmu akwai abubuwa masu yawa da sun tuna sai su firgita su ji tamkar rayuwarsu ta shiga wani haɗari."

Matthias mai shekaru 21 da haihuwa sojin Jamus da ya yi yaƙi tsawon watanni huɗu da rabi a Kundus dake arewacin Afganistan. Yana daga cikin runduna ta 19 da aka kai musu hare haren rokoki ko dai akan sansaninsu ko kuma lokacin da suke sintiri inda sojoji huɗu suka mutu. Tun a cikin watan Yulin bara Matthias ya dawo Jamus amma ya kasa komawa ga tafiyar da rayuwarsa ta da. Yanzu ya zama wani mafaɗaci kuma mai saurin fusata.

"Idan alal misali na ji ƙarar rufe ƙofa, nan-take sai in firgita in ji tamkar an harbo roka ne a cikin sansannin soji. Hakazalika idan ana yawo cikin gari ina yawan tunani ina waiwaya saboda tsoron da nake yi cewa wani na iya daɓa min wuƙa a baya. Ko da yake wannan tunani ne kaɗai amma ina jin tsoro."

Halin da sojojin ke ciki yanzu a Afganistan ya banbanta. Stefan Werdelis fada a rundunar sojin Jamus ya yi watanni huɗu yana yiwa sojoji wa´azi da kwantar musu da hankali a arewacin Afganistan ya ce bai kamata jama´a ta mayar da sojojin tamkar bare ba. Kamata yayi a riƙa gode musu da nuna gamsuwa ga gudunmawar da suke bayarwa. Ta haka za a fi samu nasarar magance matsalolin da suke samun kansu ciki bayan sun dawo gida.

Mawallafa: Sarah Steffen/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala