1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matsalolin rashin kasafin kudi a Najeriya

May 4, 2018

An kama hanyar kai wa ya zuwa barazana ga tattali arziki na mutane bayan share tsawon watanni shida ana zaman jiran kasafin kudi mafi tasiri ga gwamnatin APC mai mulkin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2xCDR
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Duk da cewar dai an dauko alkawarin farawa  tare da kaiwa ga amincewa a cikin kasafin tarrayar najeriya na shekara ta 2018 tun a watan  Janairu, ana shirin share satin farko na watan Mayu a cikin jiran kasafin Najeriya na shekarar bana.

Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Hoto: Reuters/A.Sotunde

Sau dai dai har guda uku dai ana sa ran kaiwa ga amincewar kasafin sau Ukun yana zama tatsuniyar gizo gay an majalisar da daga dukkan alamu suka dau kasafin ya zuwa makami a cikin yakin dake tsakaninsu da bangaren zartarwa.

Nigeria Präsident Muhamadu Buhari
Hoto: Novo Isioro

'Yan majalisar dai Allal misali sun sa kafa sun watsar da batun kasafin domin wata ziyara ta musaman ga  senata Dino Melaye da ya shiga takun saka da hukumar yan sanda ta kasar.

Tun kafin nan dai dama majiyoyin fadar gwamnatin kasar na zargin kokarin neman amfani da  kasafin kudin kasar a matsayin makamin neman tsayar da siyasar shari'ar shugabannin majalisar dattawan Bukola Saraki. A  fadar Aliyu Sabi Abdullahi da ke zaman kakakin majalisar dattawa batun kasafin hurumi ne na wakilcin da babu gaggawa.