Matsalolin gina massalatai a Amurka: | Zamantakewa | DW | 09.01.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalolin gina massalatai a Amurka:

Har yanzu dai babu wani takamaiman adadin musulmi dake zaune a kasar Amurka sabada babu wasu alkalluma da hukuma ta tanadar na tattarawa yawan su.

Aza harsashen gina masallaci a Berlin

Aza harsashen gina masallaci a Berlin

Da yawa daga cikin muslmin Amurka ‚ya’ya ne da jikokin wadanda suka fito daga kasashen musulmi daban daban na duniya dake suka yi kaura zuwa Amurka inda kashi daya cikin ukun musulmin kasar ke Amurkawa ne bakar fata. Kamar yada suke a nan kasashen turai a Amuzrka ma ana samun karuwa wajen gine- ginen masallatai a cikin yan shekarun baya bayan nan. Idan kun biyo mu a hankali zakuji karin bayani a cikin shirin na yau.

Omar Khalidi kwarraren masanin ne na tsara gine ginen masalaci a Amurka, ya kara mana haske akan irin matsalolin da musulmi ke fuskanta wajen aikin gina masalaci:

Babban matsala shine gamayya musulmi na bukatan kudi wajen gina massallaci, wannan shine babban barazana da ake fuskanta, bayan hakan babu wani matsala a game da dokoki dakan iya kawo cikas wajen gine ginan massalatai, kuma babu wata matsala daga hukuma da kann iya hana gina masallatai, kowai matsala a nan shine samun tara kudin da zai isa gina manyan masallatai masu kwari.“

Idan dai ana batun ne game da aikin gina masalaci to babu wani banbanci daga ire iren wahalolin da musulmin a Amurka da kuma takwarorin su a turai ke fuskanta inji Omar Khalidi, wannan kwarrare wajen tsara sampurin gina masalaci. Ko da yake gwamnatoci a kasashen yamma na tabbatar da ‘yancin musulmi wajen ba su damar gina masalaci, amma sau da yawa al’umomi musulmi da kan su ke samar da kudin tafiyar da wannan aiki na gine ginen massalaci. Kamar yadda yake a nahiyar turai, a Amurka ma ada musulmi sukan yiwa tsafin gidaje ko ofisoshi kwaskarima su sake musu fasali don mayar da su wuraren ibada. Hakan kuwa ya samo asali ne tun a farkon karni na 20 lokacin da musulmi yan cin rani daga yankin da yanzu ya zama kasashen Syria da Lebanon, Jordan, Israila da Palestin, suka fara yin kaura zuwa kasashen ketare. Amma sai a cikin shekarun 1960 ne aka fara mayar da hankali wajen gina masallaci kamar yadda aka sani a yanzu hakan a kasashen larabawa. A halin da akae ciki yanzu dai akwai masallatai sama da dubu biyu a Amurka, Bincike ya nunar da cewar, da yawa daga cikin masalatan an gina su ne daga cikin shekaru talatin da suka wuce.

A Amurka kuwa musulmi na anfani da salon gina masalaci har guda uku. Na farko shine wanda aka saba bisa al’ada a kasahen musulmi wanda ke tunawa musulmin da yanayin gida, na biyu kuwa ya kasance akan wani sabon tsari dake da dangantaka da tasrin gine-gine a Amurka, sai na uku da ke daukan sampurin gine-ginen zamani.

Ana son a nuna wani tsari ba kawai wanda ke da alaka da irin tsarin gine ginen Amurka ba, ko kuma wanda ke da dangantaka da al’adu ba, kana son nuna iyawa da gwanninta wanda zai yi dai dai da zamanin da ake ciki yanzu a karni na 21, ta la’akari da abinda zamani, da yanayi ke ciki. Buku da kari dole ne ka yi nazari da irin ma’akata da zasu gina masalacin, da kuma yawan kudin da aka tara da unguwa inda ake san gina wannan masallaci, duk wadannan abubuwa ne da ya kamata a mayar da hankali kan su kafin a fara aikin gina masallaci. Bayan haka ne zaka yi tunanin irin sallon da kake da shi wanda zai kara kawata masallacin domin kuwa addinin musulunci addini ne mai rayuwa, addini ne mai tafiya da canje canje na zamani, wadannan su ke tabbatar da kwarin gwiwa kuma ke tuna mana da kasar da muka fito.”

Wasun su ma baza ka gani cewar masalatai ne ba saboda basu da hasumiya da aka saba gani a bisa al’ada ajikin ko wani masalaci. Yawanci wadanda nauyin gina sabin masalatan ya rataya a wuyansu, kungiyoyin musulmi ne masu sasaucin ra’ayi dake zaman ‘ya ‘ya ko jikokin musulmi da aka haifa kuma suka girma a Amurka ne. Ada a lokacin da iyaye da kaknni da suka fara yin kaura a Amurka, sun fi sha’awar tsarin gina masalaci irin na gargajiya wandanda aka saba da su bisa al’ada. Omar Khalidi wanda asalin dan kasar Indiya ne, yace a gare shi ko shakka babu cewar sabon tsarin na gina masalaci da suka kirkiro a Amurka zai samu karbuwa nan gaba.

Muna son mun banbanta Musulunci daga wasu al’adu irin na masu tsatsauran ra’ayi, wannan ba abinda muke bukata a nan ba ne, wata kila wannan al’adar ta samu kabuwa a wadannan wuraren, amma nan bamu bukatar ire iren su, don hakan ina son in kirkiro wani tsari wanda yayi dai dai da al’adu da aka san Musulunci da su a nan Amurka. Ba inda aka ce dole ne Musulmi ya kasance mai cimaka irin na larabawa ba, ko kuma ya saka kaya mai alaka da larabawa ba, imani a zuciya yake, ina son inyi addini kamar yadda yake a Amurka da nan Jamus da kuma sauran kasashen turai.”

A nan Jamus kuwa, wata kungiyar musulmi ta aza harsashi na gina masallaci a kudancin birnin Berlin domin nuna adawa ga tsare tsaren gwamnati wadda ke dari dari wajen shigar da musulmin kasar da yawan su ya zarce miliyan 3.2 a cikin harkokin gwamnati. Ana sa ran cewar za’a yi bukin bude masallacin mai suna Ahmadiya Movement Mosgue, mai rufi da kuma tsawon mita fiye da 12 na hasumiya da ake ginawa yanzu hakan a wani wuri da ada ake noman ganyayyakin abinci, kusa da garin Pankow-Heinersdorf a shekara mai zuwa. Amma yin hakan ya jawo bacin rai daga al’uman garin wadanda suka koka da cewar yawan musulmi dake zaune a garin bai kai ya kawo ba da har za’a gina masallaci a wurin ba. Wajen mutane 40 masu dauke da katutuka kuma suna ta fadin cewar, Ba mu son masallaci a Pankow, suka yi zanga-zangar ruwan sanyi a sansannin inda ake aza harsashin masalacin. Shugaban masu fafutukan gannin an hana gina wannan masallaci a garin, Joachim Swietlik, cewa yayi, kamata yayi duk gine gine irin na addini ya kasance a tsakiyar gari inda mabiyan addinin suke da runjaye. Ya kara da cewar Kungiyar Ahmadiya wadda ta samo asalin ta daga Indiya, kuma mai tsautsauran matakai, kungiya ce wadda ke adawa da tsare tsaren demokradiya. Kungiyar mai yawan mambobi dubu 30,000 da masallatai 15 a wurare daban daban cikin wannan kasa ta sake nanata matsayar ta akan zaman lafiya. A lokacin da ake bukin aza tubalin gina masalacin sai da aka kawata wurin da katutuka masu dauke da rubuce rubuce dake cewar, Musulunci addini mai son zaman lafiya da kwanciyar hankali. Daya daga cikin jami’an dake kula da gina masallacin Ahmadiya, mai suna Abdullah Uwe Wagishauser shi ma kansa Bajamushe, yace ba su taba samun matsala da mutanen dake zaune a sauran wuraren da aka gina sauran masallatai 15 dake nan kasar ba, kuma masallacin su na taimakawa wajen kara hada kan jama’a da kuma kara halin cudanni in cudeka tsakannin mutane. Jin kadan kafin bukin kirstimeti ne Hukumomin a Berlin suka bada izinin gina masallacin, bayan da akayi wata daya ana kai ruwa rana tsakannin jami’an da gwamnati. Musulmi a Berlin sun koka da rashin goyan bayan gwamnati wajen shigar da su a cikin al’amuran ta. Matsalolin da ake fuskanta a yanzu hakan game da gina masalacin ya bayyana a fili irin wahalolin da musulmi ke fuskanta daga al’uman kasar. Daman yawacin musulmin dake zaune a kasar ta Jamus ‘yan asalin turkiya ne wadanda da yawan su masu aikin hannu ne da suka yi kaura zuwa Jamus bayan yakin duniya na 2. Abdul Basit Tariq, limamin masallacin Ahmadiya ya shaidawa kamfannin jaridar Reuters cewar yana bukatan babban masallaci domin karuwa da ake samu na musulmi masu sallah a masallacin. Sabon masallacin na Ahmadiya zai iya daukan yawan mutane 250 nan gaba idan an kammala gina shi. Ana sa ran bude massalacin ga jama’a musulmi a cikin shekara mai zuwa idan Allah Ya kai mu.

 • Kwanan wata 09.01.2007
 • Mawallafi Rabi Gwandu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvT5
 • Kwanan wata 09.01.2007
 • Mawallafi Rabi Gwandu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvT5