Matsalolin da baki mata ke fuskanta a kasashen nahiyar Turai | Zamantakewa | DW | 21.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalolin da baki mata ke fuskanta a kasashen nahiyar Turai

Mata baki a kasashen Turai sun yi kira da a girmama ´yancinsu

default

Ministan cikin gida na Jamus,Wolfgang Schäuble

Alkalumma sun yi nuni da cewa mata sun kai kashi 52 cikin 100 na yawan baki dake zaune a nahiyar Turai baki daya. Yayin da a hannu daya wasu matan ke yin kaura na radin kansu inda suke yanke shawarar zuwa wata kasar waje don zama na wucin gadi ko na dindindin. A daya hannun kuwa wasu kasuwannin kwadago na kasa da kasa ke samar musu da aikin yi a waje a fannoni daban daban kamar na yiwa maza hidima ko aikace aikace na gida. To sai dai sau da yawa ana tilasta musu yin irin wadannan ayyuka ne, inda ake cin zarafinsu musamman wadanda ba su da takardun izinin zama cikin wata kasa. To sai dai a nan Jamus alal misali ba kowa ne ya san irin mawuyacin halin da wadannan bakin ke samun kansu a ciki ba. Saboda haka a karshen makon jiya a birnin Kolon aka gudanar da wani taron wayarwa da jama´a kai mai taken kare ´yancin baki mata da nufin fito da irin wannan cin zali da ake musu a bainar jama´a. Idan kun biyo mu a hankali zaku ji karin bayani a cikin shirin na yau wanda ni MNA zan gabatar.

Baki mata na tallafawa ´yan´uwansu baki mata, wannan dai shi ne abin da ya fi daukar hankali a gun taron. A gun wannan taron dai mata ne suka gabatar da jawabai akan halin da baki mata ´yan ci-rani suke ciki amma ba ´yan siyasa da masana ilimin kimiyya ba. Kimanin kashi 80 cikin 100 na mahalarta taron daga kasashe kusan 24 masu tarihi daban daban. Kowace daga cikin su kuwa masaniya ce akan halin da take ciki da matsalolin da take fuskanta a tsakanin al´umar Jamus fararen fatu. Kungiyar dake kula da harkokin mata baki ta birnin Kwalan, da ake kira agistra ta shirya wannan taro. Shugaban taron Jae-Soon Joo-Schauen ta yi bayani tana mai cewa.

“Ba safai ne mata baki ke haduwa irin haka, domin tattaunawa akan bukatunmu da sauran batutuwan da suka shafe mu ba. Kasancewar mu tsiraru a nan Jamus, a kullum muna fuskantar wariya iri daban-daban. Saboda haka ya na da muhimmanci daga lokaci zuwa lokaci muna shirya irin wannan taro don daga muryar mu sama.”

Matahalarta taron sun kuma tattauna akan shigar da mata cikin harkokin siyasa da samun wata kyakkyawar kafa ta tuntubar juna. Wani misali a nan shi ne rahotannin da gwamnatin tarayyar Jamus ke gabatarwa MDD a ko da yaushe, wanda a ciki take bayani kan yadda take aiwatar da kudurorin kasa da kasa na yaki da wariyar launin fata da wariyar jinsi. Kungiyoyi masu zaman kansu kan yi duba tare da yin tsokaci akan irin wadannan rahotannin da a lokuta da dama ba sa tsinana komai.

Matan dai na son a sakar musu da mara da ba su damar daukar makomar su da kansu a cikin wata al´uma da bakin suka kira wai bakuwa, duk da cewa da yawa daga cikinsu sun shafe shekaru da dama a Jamus ko kuma a nan aka haife su. Matsalar nuna wariyar ba ta tsaya akan baki mata ko ´yan gudun hijira kadai ba, a´a ta kuma shafi dukkan matan da launin fatarsu ya fita daban wato kamar ´ya´ya tsakanin Jamusawa da ´yan Afirka ko ´yan Asiya. Eleonore Wiedenroth-Coulibaly ta kungiyar bakaken fatu a Jamus cewa ta yi.

“Hakin dan Adam ya shafi duk wani ´yanci da ya kamata a bawa mutum da kuma nauyin da ya rataya kansa. Abin da ya fi tayar mini da hankali shi ne yadda ake tauye ´yancin fadar albarkacin baki, ´yancin samun aiki da na taimako daga hukuma. Dukkan wadannan na kunshe a cikin hakin dan Adam.”

Ba safai ne baki mata ke daukar hankalin kafofin yada labarun Jamus ba. Kusan a kullum ana yi musu kyallon wadanda ake yin fataucinsu ko yi musu auren dole ko cin zarafinsu iri dabam dabam. Wannan batu bai taka wata rawar a zo a gani a gun taron ba. Irin kalaman da aka yi amfani da su a gun taron ya nunar a fili yadda ra´ayin baki mata ya bambamta da na shugabannin siyasar wannan kasa. Selmin Chaleshkaan ta wata kungiyar mata da ake kira Medica Mondiale ta yi nuni da cewa.

“Da na jin an ambaci kalmar nan ta sajewa sai tsigar jikina ya tashi. Shin wane ne ya kamata ya saje da wani? Kullum sai a ce baki ya kamata su saje da al´umar Jamus, to amma ban sani ba shin su wane ne al´umomin Jamus? Su ma fa sun bambamta. A gani dole ne su ma wadanda ke da rinjaye su saje a cikin wata al´uma mai al´adu daban-daban. Dole ne a bamui ´yanci daidaiwa daida.”

Kusan shekara guda kenan da Jamus ta kafa dokar yaki da wariya da nuna bambamci. Wai shin wata ma´ana matan suka bawa dokokin kasa da kasa da suka shafi baki? Wannan dai shi ne batun da Manuela Boyadjiyeff masaniyar zamantakewa a birnin London ta yi magana kai. Ta ce a hannu daya mata na taka muhimmiyar rawa wajen sajewar baki a cikin al´umar sannan a daya hannu suna taimakawa ´yan´uwa da suka baro su a kasashensu na asali. ´Yan mulkin mallaka sun ci da gumin kasashen da daukacin baki matan suka fito. Sannan yanzu masana harkokin zaman baki na tunanin tilastawa wadannan baki tura wani kaso na kudaden da suke samu a kasashe masu arzikin masana´antu don gudanar aikin raya kasashensu.

Ta ce “Yanzu kokari ake a hada kan wadannan mutane domin a dora musu nauyin sake gyara wuraren da ayyukan ´yan mulkin mallaka suka yi sanadiyar lalacewarsu.”

Wannan taron dai ba zartas da wani kuduri bayan taro ba. To sai dai abin da suka sa gaba shi ne zasu karfafa tuntubar juna a fannoni da dama. Duk da goron gayyatar da suka turawa dukkan ´yan siyasar Jamus, jam´iyar The Greens da ta masu neman canji kadai suka aike da wakilansu a ranar karshen ta taron. Ko shakka babu da jam´iyun dake jan ragamar mulki a kasar nan sun amfana kwarai da gaske da batutuwan da aka tattauna a gun taro.