1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

matsalolin bakin haure a nahiyar Afrika

November 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bud4

Ƙungiya kasa da kasa mai kulla da kyautata rayuwar al´umma wato CISP, da ke cibiyar ta a Italia, ta bayyana rahoto a game da halin da baƙin haure ke ciki, a wasu ƙasashen Afrika.

A tsawan watani da dama, kungiyar ta gudanar da bincike a ƙasashen Niger, Mali, Senegal,Mauritania, Algeria da Marroko.

Ta gano cewar, akwai a ƙalla bakin haure, dubu 15 da ke gararamba, bayan an haramta masu shiga turai ta ɓarauniyar hanya.

A halin da ake cikin wannan matasa sun shuiga halin basu ga tsuntsu ba su ga tarko.

Wato bayan sun kasa shiga turai , sun kuma ƙi komawa ƙasashen su na assuli.

Shugabar ƙungiyar CISP, ta yi kira ga gwamnatocin ƙasashen turai, su gaagauta samar da tallafi, ga wannan matasa , domin ita ce hanya ɗaya, da z ta basu damar neman na kansu, a Afrika, ƙila har ma su manta, da burin su na zuwa turai.

A ƙarshe, rahoto ƙungiyar, ya ƙiyasta cewar, daga shekara ta 2000 tzuwa 2005, kimamnin bakinhaure dubu 3 su ka rasa rayuka, ko dai cin ruwan teku, ko kuma cikin hamadar Sahara , a yunƙurin su, na shiga turai, da su ka ɗauka a matasyin tudun mun tsira.