1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin aikin Hajji a Najeriya da Nijar

Mahaman Kanta AH
August 23, 2017

A shekarar bana mutane da dama ne ba za su samun yin aikin hajji ba a Najeriya da Nijar, duk da cewar sun riga sun biya kudadensu amma kuma har yanzu ba su samu tafiya ba.

https://p.dw.com/p/2iiZ0
Terror-Anschlag in Mekka Verhindert
Hoto: Getty Images/AFP/B. Aldandani

Misali a Nijar mutane kamar dubu uku ne har yanzu suke jibge a filin jirgin samar birnin Yamai suna jiran gawon shannu, bayan sun riga sun biya kudadensu amma har yanzu jiragen da za su kwashe mutane sun gaggara. Yayin da a Najeriya ma a wasu Jihohin irin su Bauchi da Adamawa aka samu karancin jirangen saman domin kwashe maniyantan zuwa kasa mai tsarki. Hakan na zuwa ne daf da lokacin da ake shirin rufe karbar maniyanta a kasa mai tsarki.