1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar zaɓen Sudan

March 19, 2010

Cibiyar nazarin harkokin siyasar ta Jimmy Carter ta wallafa wani rahoto inda ta bukaci a ɗage zaɓen watan Agrilu a Sudan saboda ya na cike da kura-kurai.

https://p.dw.com/p/MXpH
Shugaba Al Bashir a lokacin gangamin siyasaHoto: AP

Cibiyar ta jimmy Carter ta na ci gaba da nuna fargabarta game da rikice rikice da ke kunno kai a wasu sassa na yammacin Sudan duk da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da ɓangarorin da ke gaba da juna suka cimma. ko a wannan jum´ar ma, rikici tsakanin makiyaya da kuma dakarun gwmanati ya haifar da salwantar rayuka 13 a yankin ƙasar da ke da arzikin man fetur. Makamancin wannan tashin tashina da kuma kame wasu yayan ɗaya daga cikin ƙungiyoyin yan tawayen Darfur, a cewar rahoton da cibayar ta wallafa, ya na iya ruruta wutan rikicin siyasa. A saboda haka ne cibiyar ta nemi hukumomin Khartum da su ɗauki matakan kawo ƙarshen fito na fito tsakanin ɓangarorin daban daban musamman ma a yankin Darfur. Hakazalika cibiyar ta tsohon shugaban na Amirka ta nemi hukumomin Khartum da suka soke dokar da ta ke taƙaita zirga zirga domin bai wa yan takara damar gudanar da gangamin siyasa.

Symbolbild Wahlen Sudan
Shirin Zaɓe mai kura-kurai a Sudan

Graham Elson da ke zama shugaban reshen cibiyar Carter ta Sudan ya ce matikar ba a cika waɗannan sharuɗan ba, to Sudan za ta iya gwamace kiɗa da karatu.

" ya ce a halin yanzu babban ƙalubalen da ke gabansu shi ne na magance ƙarancin kayayyakin da ake bukata don gudanar da zaɓe mai inganci. A gani na ana bukatan ƙarin lokaci domin ɗaura wannan ɗamarar tinkarar zaɓen na gama gari kasancewa ƙasar ba ta naƙalci yadda ake shirya zaɓe ba. A yanzu haka daidai da mitocin da aka tanada don raba akwatunan zaɓe sun yi kaɗan. A taƙaice dai da akwai bukatar ƙara kintsawa."

Rabon dai ƙasar ta Sudan ta shirya zaɓe imma na shugaban ƙasa ne ko ma dai sauransu ne tun shekaru 24 da suka gabata. Sai dai a halin yanzu yaƙin neman zaɓen da aka fara tun kwanaki shidan da suka gabata na tafiya salin alin tsakanin yan takara dubu 16 da ke zawarcin kujerun majalisa 1841. Sai dai wasu jam´iyu na cewa ba bukatar ɗage zaɓubbukan domin zai iya rusa jadawalin da aka tsaida na shirya zaɓen jin ra´ayin jama´a da aka tanada a kudancin Sudan a shekara ta 2011. Ko ma dai ya za ta kaya dai.

Graham Elson ya ce da akawi bukatar sara ana duban bakin gatari ga yan takara.

"Ya ce muna bai wa yan takara shawarar su nuna halin ya kamata tsakaninsu tare da gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin yanci da walwala. Ita kuma gwamanti ta sakar ma kowa mara gudanar da gangami ako ma ina cikin Sudan.Ta wannan hanya ce za a iya mutunta hakkin kowa da kowa. Kuma a asassa zaman lafiya da kwanciyar hankali."

Sudan Demonstrationen
Gangamin yakin neman zaɓeHoto: AP

Rahotannin da suke fitowa daga birnin Khartum sun nunar da cewa runfunan zaɓe da aka tanada sun yi ƙaranci idan aka kwatata da mutanen da suka yi registan zaɓe. Uwa uba kuma yan takara na bukatan izini daga hukumomi kafin su yi amfani da kafafen watsa labarai domin yaɗa manufofin jam´iyunsu. A saboda haka ne Cibiyar Catar ta nunar da cewa kitso ake nema a yi akan ƙwarƙwata domin kura-kuran da aka tafka a shirye-shiryen zaɓen na Sudan na iya haifar da sabon rikici maimakon mayar da ƙasar kan turbar demokarɗiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Halima Abbas