1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar yunwa a kudancin Afrika

matsalar yunwa

matsalar yunwa

Ga jama’ar kauyukan dake kudancin Mozambique,karancin abinci na wannan shekara shine mafi muni da zasu iya tunawa a cikin shekaru da dama da suka shige.Sai dai maaikatan agaji sun baiyana tsoronsu cewa mai yiwuwa ne kasashen duniya ba zasu hanzarta kaiwa agaji ga kasar ba har sai abin ya kai ga wani mummunan matsayi.

A kudancin Afrika inda majalisar dinkin duniya tace kusan mutane miliyan 10 mafi yawansu masu fama da cutar kanjamau da kuma kangin talauci, a yanzu haka suna fuskantar bala’in yunwa nan da karshen wannan shekara.

Maaikatan agaji sun yi kashedin shiga cikin hali irin wadda jamhuriyar Nijar ta fada inda mutanenta kusan miliyan 3 da dubu dari 6 suke fusakantar karancin abinci.Kasar Nijar din ta samu gudumowa daga kasashen duniya sakamakon yayata halin da ta ke ciki ne da kafofin yada labarai suka yi.

Kodayake a kasar ta Mozambique wasu yankuna suna samun ruwan sama sosai, hakazalika wasu suna anfani da salon noma wadda suka gada daga yan mulkin mallakar kasar wato Portugal domin inganta samarda abinci.

Amma a lardin Guija mai tazarar kilomita 200 daga bababan birnin kasar Maputo,kashi 2 ne cikin dari na anfanin gona da aka girbe a watan Aprilu za’a iya anfani da shi saboda saura sun lalace.

Matsalar karancin abinci ba Mozambique kadai ta tsaya ba, domin kuwa a yawancin kasashe makwabta kamar,Zimbabwe,Zambia da Malawi nan ma suna fuskantar karancin abincin ,inda yawancin iyali basu adana wani abinci ba saboda rashin kyan damina.Hakazalika ga cutar kanjamau da ta kara munana halin da ake ciki musamman ma a kasashen Swaziland da Lesotho.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin duniya WFP ,ta baiyana hadewar bala’o’in uku, talauci da ,karancin abinci da kuma cutar kanjamau a kudancin Afrika cewa shine mafi muni da aka taba fuskanta a duniya.

Mataimakiyar shugaban hukumar samarda abinci ta MDD a Mozambique Karin Manente ta ce akwai wasu matsaloli yanzu a duniya,inda ta bada misali da matsalar da Nijar take ciki ,ga Darfur ga kuma tsunami wadda ta ce da wuya a samu isassun kudi da ake bukata don taimakawa Mozambique.

Cikin dala miliyan 256 da hukumara ta ke bukata don magance matasalar ta Mozambique daga nan zuwa watan yuni na shekara mai zuwa, a yanzu haka dala miliyan 158 kacal take da su.

Ya zuwa yanzu rahotanni sun ce mutane 12 sun rasa rayukansu saboda rashin isasshen abinci,a lardin na Guija inda anfanin gona ya bushe.

A wani kauyen a cewar wani maaikacin agaji Sam Kaijuka yara kanana suna barci a azuzuwansu a kowane lokaci saboda burkutu da ake dura musu da dare domin ya rage ciwon yunwa da suke fama da shi.

 • Kwanan wata 11.08.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvaW
 • Kwanan wata 11.08.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvaW