1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yunwa a kudancin Afrika

Hauwa Abubakar AjejeOctober 7, 2005

Hukumomin agaji sun fara wani sabon yunkuri na magance mataslar yunwa da ta bullo a kudancin Afrika

https://p.dw.com/p/BvZ3
Hoto: AP

Rashin ruwan sama,da balain cutar kanjamau,sun mayarda kudancin Afrika,yanki na baya bayannan daya shiga mataslar yunwa a nahiyar Afrika.

Gwamnatoci da hukumomin bada agaji sun ruwaito cewa,kimanin mutane miliyan 12 ne zasu bukaci agajin abinci na tsawon watanni shida kafin lokacin girbi na shekara ta 2006.

Kakain yanki na hukumar samarda abinci ta Majalisar Dinkin Duniya,Mike Huggins,yace hukumar tana bukatar kusan dala miliyan 400 domin ciyarda mutane akalla miliyan 9 da dubu 200 da suke fuskantar yunwa.

Kakakin hukumar,Huggins, ya kara baiyana cewa kudin da hukumar abincin take bukata ya gaza da kimanin dala miliyan 180,duk kuwa da gargadi da hukumar tayi na wattani na Karin kudaden.

Yace rashin isasshen kudin zai shafi mutane da dama dake fama da yunwa.

Rashin isashen ruwan sama a wasu sassa na yankin,ya sanya mafi yawa na masara da aka shuka basu fito ba, ko wasu kuma sun bushe,musamman a kasar Zimbabwe wadda ada can take tunkaho da isashen anfanin gona.

Kodayake shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe,ya dora laifin karancin abincin dama matsalar tattalin arzikin da kasar ta shiga yanzu, akan takunkumi da kasar Burtaniya ta shirya saboda manufar gwamantin Zimbabwe ta kwace gonakin fara fata yana baiwa bakar fata na kasar.

Wani balai kuma shine na cutar kanjamau a yankin na kudancin Afrika,inda cutar take kashe da yawa daga cikin masu aikin gona, wasu kuma basu da isashen lafiya da zasu iya tabuka wani abu ko neman abincin da zasu ci.

Matasalar rashin abinci mai gina jiki sai karuwa takeyi a kasar Malawi,inda a yanzu haka kusan mutane miliyan 5,wato kusan rabi na jamaar kasar ta Malawi,wadda take daya daga cikin kasashe mafiya talauci a nahiyar Afrika,suke matukar bukatar abinci.

Rahotanni sun nuna cewa tuni da yawa suka mace saboda cin wasu ganyaye da tsirrai masu guba, dalilin yunwa da rashin abinci.

Kwararru wajen wani babban taro akan matsalar yunwa a Zimbabwe,sunyi gargadin cewa, mutanen da basu samun abinci mai gina jiki,sunfi sauran jamaa hadarin kamuwa da cuttuka,dake kashe akalla yan afrika dubu 700 a kowace shekara.

A wani rahoto da ta bayar,hukumar agaji ta Red Cross,tace tana bukatar dala miliyan 27 cikin gaggawa,domin taimaka ciyar da mutanen da suke matukara bukatar abinci a kasashen Lesotho,Malawi Mozambique,Namibia,Swaziland,Zambia da Zimbabwe.

Kodayake hukumar ta Red Cross ta nuna damuwarta cewa, kasashe da kungiyoyi masu bada agaji zasu gajiya, da bada taimakon musamman bayan matasalar kasar Nijar inda har yanzu yara kanana suke fama da yunwa duk kuwa da taiamako da aka samu a kasar.

Halin da nahiyar Afrika take ciki,ya samu fifiko gaban shugabannin kasashen duniya,wadanda suka amince a watan yuli daya gabata cewa,zasu kara yawan taimako tare da yafewa wasu kasashen Afrika basuka da ake binsu.

Sai dai kuma hukumomin agaji sun baiyana tsoronsu cewa,mai yiwuwa ne jamaar dake zama a kasashen da suka ci gaba zasu gaji da kallon hutunan yan Afrika talakawa da suke fama da yunwa ta akawatunan telebijin dinsu.

Kodayake,shugababn sashen nazarin hulda da jamaa na jamiar kasa da kasa ta Witwatersrand,John Stremlau,ba haka yake ganin abin ba,domin kuwa a cewarsa,idan kafofi yada labarai musamman gidajen telebijin sun ci gaba da nuna hotunan wadanda suke fama da yunwa,jamaa da dama zasu farga su kuma matsawa gwamnatocinsu, gagguta bada taimako ga wadannan kasashe.