1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar yaduwar murar tsuntsaye

Hukumomin Nijeriya sun aike da wani samfurin jini daga wasu ´yan gida guda da suka yi zargin yana dauke da nau´in murar tsuntsaye mai kisa zuwa ketare don a yi gwajinsa a tabbatar ko kwayoyin cutar ya yadu zuwa ga bil Adama. Har in dai haka ta tabbata, to zai zama karon farko ke nan da dan Adam ya kamu da nau´in H5N1 a nahiyar Afirka. Wani jami´in kiwon lafiya a Nijetiya ya ce wasu yara biyu sun kamu da mura a kusa da gidan gonar nan da ke Jaji, inda aka gano nau´in murar tsuntsaye na H5N1 a ranar laraba da ta gabata. Ita ma kasar Sloveniya a yau lahadi ta aike da wani sampur na kwayoyin murar tsuntsaye na H5 da aka gano cikin wata agwagwar ruwa zuwa Birtaniya don yin gwaji a ga ko sampur din na dauke da nau´in H5N1 mai kisa. Hakan kuwa ya zo kwana guda kacal bayan da aka gano nau´in H5N1 din a cikin wassu agwagin daji a kasashen Italiya, Girika da kuma Bulgariya. Wannan dai shi ne karon farko da aka samu bullar cutar a cikin kasashen KTT.