Matsalar yaduwar masassarar tsuntsaye a Turkiya | Labarai | DW | 08.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar yaduwar masassarar tsuntsaye a Turkiya

Hukumomin Turkiya sun ce matsananciyar murar tsuntsaye na ci-gaba da yaduwa a cikin kasar, bayan an gano cutar a cikin wasu matattun kaji a jihohi biyu dake arewa maso yammacin kasar. Hakan dai ta zo ne bayan rahotannin da aka bayar cewa a karo na 4 dan Adam ya kamu da kwayoyin cutar a wani kauye dake gabashin Turkiya. To sai dai ba´a sani ba ko mutumin wanda shi ne na hudu da ya harbu da kwayoin cutar na dauke da nau´in H5N1, wanda yayi sanadiyar mutuwar wasu yara biyu ´yan´uwan juna a wani asibiti a makon jiya. Sakamakon binciken da aka gudanar akan wata yarinya da ita ma ta rasu bai tabbatar da nau´in kwayoyin na H5N1 ba. Wannan dai shi ne karon farko da ´yan Adam suka rasu sakamakon murar tsuntsayen a wajen nahiyar Asiya, inda akalla mutane 70 suka rasu sakamakon kamuwa da cutar tun bullar ta a shekara ta 2003.