Matsalar Yaduwar Kananan Bindigogi A Duniya | Siyasa | DW | 23.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar Yaduwar Kananan Bindigogi A Duniya

Kungiyar BICC dake nan birnin Bonn na daya daga cikin kungiyoyi na kasa da kasa dake fafutukar shawo kan barbazuwar kananan bindigogi a duniya

Alkaluma da aka bayar sun nuna cewar kimanin ire-iren wadannan makamai miliyan dubu 600 suka barbazu a sassa dabam-dabam na duniya kuma su ne suka fi illa ga makomar rayuwar jama’a. An yi shekaru da dama MDD na bakin kokarinta wajen hana yaduwar wadannan makamai, musamman, a kasashen Afurka da na Asiya. Misali a kasar Kamboja tuni aka kawo karshen yakin basasarta, amma gwamnati na fama da matsaloli wajen kwance damarar daidaikun mutanen dake mallakar kananan bindigogi wai domin kare kansu a wannan kasa. Da farko dai kasashen Turai sun amince da ba wa ‚yan sanda da jami’an tsaron kasar Kamboja horo bisa sharadin kwance damarar makamai da daidaikun mutane masu zaman kansu ke mallaka a kasar ta Asiya. A karkashin wannan mataki an lalata kananan makamai da yawansu ya kai dubu 130 a kasar a cikin shekaru hudu da suka wuce. An gabatar da shirin kone makaman ne a bainar jama'a ta yadda za a kwantarwa da mutane hankalinsu game da cewar ba an kwace makaman ne domin sayar da su ga wadansu ba. Amma ita Kamboja tamkar misali ne a game da yaduwar kananan makamai da kuma yadda za a shawo kan matsalar. To sai dai kuma da wuya a iya tinkarar lamarin a yankunan da ake ci gaba da fama da rikici a cikinsu. Misali a kasashe da dama na nahiyar Afurka ana ci gaba da fasa kwabrin makamai, inda a wasu yankunan akan sayar da su akan farashi mai rahusan gaske. Kungiyar BICC dake nan birnin Bonn na daya daga cikin kungiyoyi na kasa da kasa dake dake fafutukar murkushe yaduwar kananan makamai a duniya. Kungiyar tayi tsawon shekaru goma tana ba da shawara ga MDD da KTT. A lokacin da yake bayani darektan kungiyar Peter Croll yayi nuni ne da cewar ainifin dalilin yaduwar kananan bindigogin shi ne fargabar dake tattare a zukatan mutane dangane da makomar rayuwarsu, ko kuma a takaice matsalar fatara tana taka muhimmiyar rawa a wannan batu. A misalin shekaru hudu da suka wuce ne kasashen Afurka suka tsayar da shawarar daukar wani mataki bai daya tsakaninsu domin shawo kan matsalar yaduwar kananan bindigogin suna kuma neman shawara daga kungiyar ta BICC. To sai dai kuma kawo yanzun babu wani ci gaba na a zo a gani da aka samu wajen wanzar da kudurin da kasashen suka cimma a Nairobin Kenya. Ita ma MDD tayi tsawon shekaru hudu tana mai tattauna maganar yaduwar kananan bindigogin a ajendar tarurrukanta, amma ita ma a nata bangaren babu wani takamaiman kudurin da ta cimma bisa manufa.