Matsalar wariya a Turai | Siyasa | DW | 14.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar wariya a Turai

Rashin cikakkun bayanai a game da matsalar wariya na hana ruwa gudu a kokarin dakatar da hare-haren masu zazzafan ra'ayin wariya a nahiyar

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce a halin da ake ciki yanzu haka kasashen Cote d’Ivoire da Guinea ne suka fi jan hankalin wadannan mayaka, inda suke ba da hadin kai ga baraden sa kai na shugaba Gbagbo a Cote d’Ivoire ko kuma ‚yan adawa da masu goyan bayan shugaba Conte a kasar Guinea. A cikin rahoton na kungiyar Human Rights Watch, wanda ke bitar matsalolin talauci da zub da jini tsakanin matasa, an nemi shaida daga tsofaffin mayakan su 60, wadanda suka taba shiga aka gwabza da su a yake-yaken basasar Liberiya da Saliyo da Guinea da kuma Cote d’Ivoire. Kungiyar tayi kira ga kungiyoyi na kasa da kasa da yi bakin kokarinsu wajen taimaka wa wadannan matasa domin su kaurace wa filayen daga a kasashen yammacin Afurka, a kuma magance musu matsalarsu ta talauci, wadda ita ce ke iza keyarsu zuwa shiga wadannan yake-yake. Ba za a iya dakatar da tashe-tashen hankulan da kasashen yammaci Afurka ke fama da shi ba, sai tare da kwance damarar makaman wadannan mayaka da kuma samar musu da wata sabuwar madogara a rayuwarsu ta yau da kullum. Sama da kashi biyu bisa uku na tsaffin mayakan Liberiya da aka tambayi albarkacin bakinsu suka ce an nemi da a dauke su a matsayin sojojin haya a kasashen Guinea da Cote d’Ivoire. Wasu bayanai da aka tara daga jami’an dake kula da makomar sojoji, matasa, wadanda ba a dade da kwance damarar makamansu ba a kasar Liberiya, sun ce, akalla tun abin da ya kama daga watan nuwamban da wuce, wasu daruruwa daga cikinsu sun zarce zuwa Cote d’Ivoire domin shiga aikin sojan haya. A wannan makon ne gwamnatin Afrika ta Kudu ta ce tana binciken zargin da ake yi na cewar Cote d’Ivoire na ci gaba da daukar sojan haya duk da yarjejeniyar da gwamnati ta sa hannu kanta a Pretoria makon da ya wuce domin kawo karshen rikicin da ya raba kasar ta Cote d’Ivoire gida biyu. Amma bisa ga ra’ayin kungiyar Human Rights Watch talauci ne ke iza keyar wadannan matasa domin kama aikin soja a wuraren da ake fama da rikici a yammacin Afrika suna masu sa rai a game da kyautatuwar makomar rayuwarsu. Wannan dai shi ne karo na biyu da kungiyar ta ba rahoto akan wannan matsala a cikin makonni biyu da suka wuce. A ranar 31 ga watan maris da ya wuce kungiyar ta ce gwamnatin Cote d’Ivoire da dauki dubban sojoji matasa a yakin da take gwabzawa da ‚yan tawaye a arewacin kasar. Amma mataimakin sakatare-janar na MDD akan al’amuran Liberiya Abou Moussa ya ce dukkan gwamnati da ‚yan tawaye ne ke amfani da sojoji yara a yakin basasar Cote d’Ivoire.