Matsalar tsaro a Guinea-Bissau | Labarai | DW | 18.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar tsaro a Guinea-Bissau

ECOWAS za ta tattauna batun tura dakaru domin inganta tsaro a Guinea-Bissau

default

Wasu shugabannin ƙasashen ECOWAS

Shugaban Nijeriya Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya sanar da cewar ƙasashen da ke cikin ƙungiyar kasuwar tarayyar yammacin Afirka ta ECOWAS za su gudanar da taron gaggawa domin duba yiwuwar tura dakaru zuwa ƙasar Guinea - Bissau, wadda ke fama ta tashin hankali. Shugaban na Nijeriya, wanda shi ne ke jagorantar ƙungiyar ta ECOWAS - mai ƙasashe mambobi 15, ya ce shugaban ƙasar ta Guinea - Bissau ne ya buƙaci ƙungiyar ta samar masa dakaru 600 domin shawo kan matsalar rigingimun da ƙasar ke fama da su.

Ana dai ganin ƙasar ta Guinea-Bissau a matsayin babban wurin da masu safarar muggan ƙwayoyi ke yada zango akan hanyar su ta zuwa Afirka daga kudancin Amirka, ko kuma zuwa Turai daga arewacin Amirkar. Masana harkokin diflomasiyya na fargabar cewar sojojin ƙasar na taka rawa wajen safarar muggan ƙwayoyin.

A tsakiyar watan satumba ne dai - a cewar shugaban Nijeriyar, taron zai gudana na ƙungiyar ECOWAS da ke da sojojin ta waɗanda ke yin ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala