Matsalar talauci tsakanin kananan yara na kara rincabewa a gabashin Turai | Labarai | DW | 18.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar talauci tsakanin kananan yara na kara rincabewa a gabashin Turai

Alkalumman da MDD ta bayar sun yi nuni da cewa kowane yaro daya cikin hudu a kudu maso gabashin nahiyar Turai da na kasashen tsohuwar TS na fama da matsanacin talauci. A cikin wani rahoto da ya bayar a birnin Kwalan, asusun taimakon yara na MDD UNICEF ya ce talauci shi ne babban dalilin da ya sa kananan yara musamman a kasashen Romania da Bulgaria, wadanda nan ba da dadewa ba za´a shigar da su cikin KTT, ke tashi a gidajen fandararrun yara maimakon a cikin gidajen iyayensu. Kasashe dake sahu na biyu a wajen yawan kananan yara dake cikin matsanancin talauci su ne Usbekistan da Tajikistan. A saboda haka asusun na UNICEF yayi kira ga gwamnatocin kasashen da abin ya shafa da su ba da fifiko akan matakan yaki da talauci tsakanin kananan yara.