Matsalar talauci a kasar Bulgariya | Zamantakewa | DW | 11.03.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalar talauci a kasar Bulgariya

Talauci ya fi shafar kananan yara na kabilar Roma a kasar ta Bulgariya.

´Yan kabilar Roma a Bulgariya

´Yan kabilar Roma a Bulgariya

Jama´a masu sauraro barkanku da warahaka, barkan mu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na MKT, shirin da ke kawo muku batutuwan da suka shafi siyasa da zamantakewa a fadin Turai baki daya. A duk lokacin da ake maganar talauci musamman a tsakanin kananan yara, hankali ya fi karkata ga kasashe masu tasowa inda ake fama da matsaloli na rayuwa iri dabam-dabam. Abin da watakila ba´a sani ba shi ne wannan matsala ta talauci ta yi katutu a wasu kasashen Turai, musamman a kasar Bulgariya wadda take sabuwar memba a cikin KTT, EU. A kasar ta Bulgariya kananan yara da matasa suka fi fama da matsalar ta talauci, wanda a dangane da haka suke neman mafaka a gidajen yara da na marayu, don samun abin sakawa bakin salati. Idan aka kwatanta da yawan al´uma yara a Bulgariya da ke zama irin wadannan gidaje sun ninka alal misali na nan Jamus har sau biyar. Wato kenan Bulgariya ce ta fi fama da wannan matsala a jerin kasashen kungiyar EU. Ban da haka yanayin zama a daukacin gidajen marayu da kananan yara a Bulgariya shi ne mafi muni. A dangane da haka wata kungiya a Jamus dake tallafawa gidajen yara a Bulgariya ke ba da taimakon kudi don inganta yanayi a gidajen tare da samarwa kananan yara wata kyakkyawar makoma ta rayuwa, kamar yadda zaku ji a cikin shirin na yau, wanda ni MNA zan gabatar.

Madalla: Yara kenan suke wasa a gidan yara da marayu na Maria Luisa dake garin Plovdiv dake kasar Bulgariya. Wannan gidan na daya daga cikin gidajen yara da yanayi zama a ciki ya tabarbare. Gidan da ke zama wani kango ya kusan shekaru 100 da aka gina shi. A shekara ta 1923 aka sake fasalin wata barga aka mayar da ita gidan marayun na Maria Luisa. Kimanin yara 14 ke kwana a cikin daki guda ba tare da sun samu wata dama ta fita daga gidan ba. Hakan kan janyo gushewar basirar wadannan yara.

Janko ke nan wata budurwa mai shekaru 16 ta ke rera wata waka mai taken Mama dake kunshe da kalamai masu sosa rai, tana mai cewa da ma a ce ina tare da mahaifiya ta ai da ba karamin jin dadi da murna zan yi ba. Yara a gidajen marayu na sha´awar wannan waka ta al´umar Bulgariya.

B: To sai dai yanzu an dan samu sauyi, domin tun bayan sabunta gidan marayun a garin Plovdiv zuwa na zamani a fadin kasar ta Bulgariya, inda kuma yanzu yara ke wasan su ba bu tsangwama ko wata fargaba game da makomar rayuwarsu. Sabbin tagwayen gine ginen guda biyu an rarraba su zuwa sassa dabam-dabam na dakunan zama, inda yara da masu renonsu ke iya tafiyar da rayuwa kamar irin wadda aka saba a gida tsakanin yara da mahaifan su.

A: Kyakkyawan yanayin da ke wanzuwa yanzu a gidan marayu na karfafa guiwan yaran musamman don hagen wani haske ga rayuwarsu, inji Darina Kukewa mai kula da gidan marayun na Maria Luisa.

„Da yawa daga cikin yaran da ke a nan wurin ba zasu iya zama da iyayensu ba saboda gana musu azaba da cin zarafin su da kuma lalata da su da wasu iyayen ke yi. Wato akwai matsaloli da yawa. Hukumomin da alhakin ba da kudin tafiyar da wadannan gidaje ya rataya a wuyansu, su din ma ba su da ko sisin kwabo a baitul-malin su. Saboda haka ba mu da isassun masu kula da yaran. Ko da yake a dangane da taimakon da muke samu daga Jamus, yanzu mun samu gidan marayu mafi kyau a Bulgaria, kuma yaran na farin ciki da haka, amma ya zama wajibi mu warware matsalolin rashin kudi da muke fuskanta ta yadda zamu iya tafiyar da aikin wannan gida ba da wani cikas ba.“

A: A Bulgariya albashin karamin ma´aikaci bai wuce Euro 150 a wata ba, yayin da farashin kaya ke daidai da na sauran kasashen yamma. A saboda haka magidanta ba sa iya daukar nauyin ciyar da iyalinsu. A lokuta da dama gidajen marayun ke zama kafa ta karshe inda yara ke neman mafaka, inji darina Kukewa.

„Akwai yara da dama dake fama manyan matsaloli. Alal misali yara biyu daga cikin wadanda muke da su a nan, sun taba rayuwa akan bola tare da karnuka da kyanwoyi, ba sa samun abinci balantana magani. Saboda haka yanzu suna fama da matsaloli na tabin hakali. Yau dai kusan shekaru 3 kenan da muka dauke su a nan, kuma ina iya cewa sun fara murmujewa.“

B: Daukacin yaran da ke zaune a gidajen marayu a Bulgariya ´yan kabilar Roma ne. ´Yan kabilar ta Roma su ne rukunin ´yan kasar na farko da suka fara asarar wuraren aikin su bayan da iskar canjin manufofin siyasa ta kada a Bulgariya a shekara ta 1989, inji Anton wanda dan kabilar Roma ne. A halin da ake ciki yana duk iya kokarin kula da ´ya´yan sa su 8, duk da cewa ba ya da aikin yi yanzu. A da Anton ma´aikaci ne a wani kamfanin kera kayan aiki, amma tun bayan da kamfani ya rushe tun a wasu shekaru baya, har yau ba sai mu aikin yi ba.

A: Anton kwararren ma´aikaci ne kuma ya na sha´awar wake wake, inda a duk yamma yake hada kann iyalin sa yana rera musu waka. Ya ce ba ya bukatar kudi wajen rera wakokin kuma a wani lokacin dadin wakar na taimakawa a manta da yunwa ciki. Yanzu haka dai da shi da iyalin sa na rayuwa ne akan kwanten abincin na wasu ´yan kasar wadanda su ma ke fukantar karancin abinci.

„A kullum bola muke zuwa tsintar abubuwan da muke rayuwa a kai. A lokutan baya bayan nan ma mu kan tarar da ´yan Bulgariya da ke zuwa kwasan dan abin da ya rage mai amfani a bola. Abin nufi shi ne ba ´yan kabilar Roma kadai ke cikibn mawuyacin hali ba, hatta wani bangare na ´yan Bulgariya sun fara jin shi a jika. A kwanakin bayan nan wani matashi ya kashe kansa saboda rashin abin sakawa bakin salati. Yanzu ya zama tamkar wani abin a do na zamani, wato gara mutuwa da a kwana da yunwa.“

daukacin yara dake gidan marayu na Maria Luisa ´yan Kabilar Roma ne. Suna nuna gamsuwar su da wannan gida musamman saboda abincin da kuma kayan sayawa da ake ba su. To amma meine ne burin su a gaba. Wasunsu sun ce suna zama ´yan sanda wasu kuma shugabannin wannan kasa. Don ganin an samar musu kyakkyawar makoma a rayuwa, mai kula da gidan Darina Kukewa ta ce nan gaba za´a fara koyar da yaran musamman matasa a cikin su sana´o´in hannu.

„A nan Bulagriya mun fi yawan yara a gidajen marayu fiye da sauran kasashen Turai. A lokacin da na fara aiki a nan yara 80 muke da su. Amma yanzu sun kai 100 kuma a kullum yawansu na karuwa ne. Ina mika godiya ta ga masu tallafa mana daga Jamus. Domin sun sake maido da annashuwa da farin ciki a cikin rayuwar mu.“

 • Kwanan wata 11.03.2007
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvSy
 • Kwanan wata 11.03.2007
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvSy