1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar Taimakon Jinkai A Nahiyar Afurka

June 23, 2004

Bayanai na MDD sun nuna cewar yankin kudancin Afurka shi ne ya fi bukatar taimakon jinkai akan sauran sassa na duniya

https://p.dw.com/p/Bvik

Wakilin musamman na MDD James Morris, wanda yayi balaguron yankin kudancin Afurka ya ce wannan yanki yana cikin mummunan hali na kaka-nika-yi fiye da sauran yankunan duniya. Ya ya ce ko da yake ya gane wa idanuwansa tabargazar da ake fama da ita a yankin Darfur, amma fa ba za a iya kwatanta lamarin da mawuyacin halin da miliyoyin mutane ke ciki a Afurka ta Kudu ba. Kasashen yankin na fama da marayu sama da miliyan hudu, wadanda suka yi asarar iyayensu sakamakon cutar Aids mai karya garkuwar jiki. A baya ga haka akwai wasu mutanen sama da miliyan biyar dake dauke da kwayoyin HIV dake haddasa cutar ta Aids. A takaice kimanin kashi 24% na illahirin mazauna yankin kudancin Afurka ne ke dauke da kwayar cutar ta HIV. ‚Yar mitsitsiyar kasar nan ta Swaziland, wacce ATK tayi mata kawanya, ita ce akan gaba inda kimanin kashi 38% na ‚ya’yanta dake da shekaru tsakanin 19 zuwa 45 da haifuwa suke dauke da kwayar HIV. Hakan kuwa na ma’ana ne cewar kasar na asarar wani muhimmin bangare na al’umarta kuma yara na girma ba tare da iyayensu ba. A baya ga cutar ta Aids daya matsalar dake addabar kudancin Afurka kuma ita ce ta fari ko kuma ambaliyar ruwa, inda akan wayi gari duk amfanin da aka noma sun lalace. Kasashen Malawi da Muzambik da Swaziland da kuma Lesotho sune suka fi fama da radadin wadannan matsalolin na fari da ambaliyar ruwa. Ita ma kasar Zimbabwe, al’amuranta na ci wa kungiyar taimakon abinci ta MDD tuwo a kwarya. Domin kuwa daga baya-bayan nan kasar ta Zimbabwe ta hana wakilan kungiyar ta MDD damar kai ziyara kasar kuma ta ce ba ta ba karbar taimakon abinci daga ketare. Gwamnatin shugaba Robert Mugabe na ikirarin cewar matakinta na sake rabon filayen noma yana samun nasara matuka ainun ta yadda kasar ba ta bukatar wani taimako daga waje. In har hasashen da gwamnatin tayi ya tabbata to Zimbabwen zata iya dogaro da kanta ba tare da wata matsala ba. Amma fa zai zama abin mamaki idan har kasar ta cimma kafar noma hatsi na yawan tan miliyan dubu da dubu dari takwas, kamar yadda tayi hasashe a wannan shekarar, idan aka kwatanta da hatsi na yawan tan dubu dari tara da tamanin kacal da ta noma shekarar da ta wuce. Wannan ci gaba zai zama wani lamari na tarihin da ba a taba ganin irin shigensa a duniya ba, in ji James Morris, wanda kuma yake tattare da imanin cewar akwai wata matsalar dake kasa tana dabo a kasar Zimbabwe, wacce kuma MDD bata da ikon warwareta. Majalisar tayi hasashen cewar kimanin kashi 50% na al’umar Zimbabwe ke bukatar taimakon abinci yanzu haka.